1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wani ɗan siyasa ya yi suka ga musulmin Jamus

August 30, 2010

Jam'iyyar SPD ta Jamus na shirin korar wani mamba nata bisa laifin yin suka ga musulmi

https://p.dw.com/p/OzZt
'Yan zanga-zangar nuna adawa da littafin Thilo Sarrazin.Hoto: AP

Komitin shugabannin jam'iyyar SPD ta Jamus ya amince da korar Thilo Sarrazin, wanda marubuci ne da ke bayyanar da ra'ayoyi masu sarƙaƙƙiya, kuma mamba na komitin shugabannin babban bankin Jamus. SPD za ta yi haka ne bisa dalilin fid da wata muhawara da ya yi akan abin da ya kira ciyar da Jamus baya da musulmi 'yan kaka gida ke yi. To sai dai kuma Sarrazin ƙaddamar da littafinsa da ya yi wa suna "German Abolishes Itself" wato Jamus ta kau da kanta da kanta ya yi, a daidai lokacin da jam'iyyar SPD ke shawarta makomarsa. Sarrazin ya kare ra'ayinsa na cewa da yawa daga ciki masu kaka gida a nan Jamus, da ba su iya rubutu da karatu ba, sun fito ne daga ƙasashen musulmi. Sai dai wannan ra'ayi nasa ya gamu da kakkausan suka daga gaggan 'yan siyasar Jamus, da suka haɗa da shugabar gwamnati, Angela Merkel wadda ta ce mai yiwuwa ne hakan ya yi barazzana ga matsayinsa na kasancewa ɗaya daga cikin shugabannin babban bankin Jamus.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Abdullahi Tanko Bala