1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wanene shugaban Afirka mafi daɗewa akan karagar Mulki?

September 30, 2009

Shugaban ƙasar Gabon marigayi Omar Bongo, shine shugaban Afirka mafi dadewa akan karagar mulki kafin rasuwarsa a watan Mayun 2009

https://p.dw.com/p/JoHj
Shugaba Umaru Yar'Adua na NigeriaHoto: AP

Tambaya ta farko a shirin namu ta fito daga hannun Lawan Musa Lawal (Abbati ) Unguwar Yari Katsina, Nijeriya, ya ce Don Allah ina son ku faɗa mini dalilin daya sa aka banbanta tsakanin majalisar dattawa data dokokin tarayya a Nijeriya, da kuma abinda yasa ba'a haɗesu wuri guda ba a matsayin majalisa ɗaya.

To, Boukari dangane da amsar wannan tambayar, na tuntuɓi Dakta Ahmadu Usman Jalingo, mataimakin shugaban jama'ar jihar Taraba, dake arewacin Nijeriya, wanda kuma ƙwararre a fannin kimiyyar siyasa.

A gaba kuma, tambaya ce daga Abdullahi Kriba a jamhuriyyar Kamaru. Malamin cewa yake, don Allah ku fahimtar dani kan Lawyoyi. Ina yawan ji, kuna faɗin Lauya mai zaman kansa, kuma da Lauya - na gwamnati. Wai akwai banbanci a tsakaninsu ne, kuma Lauwa - mai zaman kansa a ina yake samun kuɗaɗensa? To, Malam Abdullahi Jibrila, domin amsa wannan tambayar, abokin aikina Salisou Boukari ya miƙata ga Moussa Koulibali, Lauya - mai zaman kansa, kuma shugaban ƙungiyar Lauyoyi ta jamhuriyyar Nijar.

To, Saleh ko da shike a shirye shiryenmu na baya, mun amsa tambayar data shafi hanyar aikewa da saƙonni ta Twitter, amma mun sake samun tambayoyin dake neman ƙarin haske akan batun, waɗanda suka fito daga Shu'aibu Marafa Dayi, Katsina, da kuma Aliyu Mustafa Gombe, jihar Gombe a tarayyar Nijeriya.

Domin jin bayani akan tambayar, ga Abba Bashir da Fatihu Sabi'u, waɗanda suka amsa tambayar a baya:

Twitter Logo
TwitterHoto: twitter.com

Sai kuma tambayar da ta fito daga hannun Malam Sa'adu el-Haji Usmane Gidan Ruji a jamhuriyyar Nijar. Ya ce don Allah ku bani tarihin shugaba Umar Bongo na Gabon, da gaske ne ya shekara arba'in yana mulki? Kuma Matansa da ɗiyansa nawa? Boukari, kaji tambayar malamin:

An haifi Albert Bernard Bongo ranar 30 ga watan disamba 1935 a garin Lewai dake yankin Ogooue, inda daga bisani aka sake sunan garin ya koma Bongo Ville.

Albert Bernard Bongo shine dan auta a gidansu, kuma iyayansa manoma ne.

An haifesu su goma sha biyu a gidan su, kuma sunfito ne daga ƙabilar Bateke ta Congo Brazzaville, tunda a lokacin Congo Brazzaville da Gabon suna dunƙule a matsayin ƙasa ɗaya.

Ma haifinsa ya rasu yana ɗan shekara 7 sannan kuma yana ɗan shekara 12 mahaifiyar sa ta rasu.

Yayi makarantar Primary da sakandre, a Congo.

Albert Bernard Bongo yayi haɗuwar sa ta farko a 1955 da Louise Mouyabi Mounkala wadda, da itane suka samu yar su ta fari mai suna Paskaline Bongo Ondimba, a 1956.

Yayi aikin soja daga 1958 zuwa 1960 inda ya fito da galar Laptanan, sannan kuma ya kasance sojan assiri na ƙasar Faransa.

Yayi aure da Patience Dabany wata mawaƙiya yar shekara 15 a 1959 wadda ta haifa masa yaya: Ali Bongo da Abertine Amissa Bonbo, daga 1964-1993.

Ranar 4 ga watan August 1990 ya auri Edith Sassou Nguesso ɗiyar shugaba Sassou Nguesso kuma sun samu yaya biyu : Omar Denis Junior Bongo Ondimba da kuma Yacine Queenie Bongo Ondimba.

Ashekara ta 1961 ya taka rawar gani a zaɓen yan majalissun dokoki da aka gudanar a ƙasar, daga nan sai Ministan harkokin wajan ƙasar na wancan lokaci Jean-Hilaire ya yaba da ƙwazon sa, kawai sai ya sashi a cikin membobin ofishin sa.

Bayan hakane, shi kuma shugaban ƙasar na wannan lokaci Leon Mba ya gano hazaƙarsa wajan aiki, sai ya naɗashi mataimakin Darectan Fadar shugaban ƙasa, sannan a watan Octoba 1962 aka naɗashi a matsayin cikakken Darecta.

A shekarar 1965 ne aka naɗashi Ministan Tsaron ƙasa da harkokin waje kuma wakili a fadar shugaban ƙasa.

Lokacin da shugaban ƙasar Leon Mba ya kamu da wani rishin lafiya, sai shugaban ƙasar Faransa na wannan lokaci Janar Degaul, tare da Ministan sa mai kula da harkokin Afrika Jacques Foccart sukayi ruwa sukayi tsaki aka naɗa Albert Bernard Bongo a matsayin mataimakin shugaban ƙasa, dan haka, a shekarar 1966 da shugaba Leon Mba ya rasu sai kawai Bongo ya zama shugaban ƙasa, a ranar 28 ga watan Novemba 1967.

A shekarar 1968 Albert Bernard Bongo, ya kafa jama'iyar sa ta PDG (parti democratique Gabonais) wadda ta kasance itace Jama'iya ɗaya tilo a ƙasar mai mulki har ya zuwa 1990.

A shekarar 1973 Albert Bernard Bongo ya muslunta inda ya baiwa kanshi sunan alhaj Omar Bongo.

Äthiopien Gipfeltreffen der Afrikanischen Union AU Präsident Omar Bongo Gabon
Omar BongoHoto: AP

A shekarar 1990 wani yajin aikin gama gari, daya faro daga ɗaliban ƙasar,ya tilastawa Shugaba Omar Bongo shirya mahawarar ƙasa, inda daga nan ne aka soma kafa jama'iyu barkatai, da kuma sabin tsare-tsare na democraɗiya, inda ya naɗa ɗan adawar nan Casemir Oye Mba, a matsayin Praminista, amma ya yi nasarar rarraba kawunan 'yan adawar ƙasar, domin jin daɗin mulkinsa.

A ranar 6 ga watan mayu na 2009 marigayi Omar Bongo Ondimba ya ɗauki hutu, dan yayi zaman makokin matarsa Edith Bongo wadda take ɗiya ga shugaba Sasu Ngesso na Congo Brazzaville, alhali kuma ana raɗe-raɗin cewa bashi da lafiya.

Shine shugaba na biyu a ƙasar, kana yayi mulki daga ranar 2 ga watan Disamba 1967, zuwa mutuwar sa, a ran 8 ga watan Yuni 2009, a wani asibitin dake birnin Barcelona na ƙasar Spain.

Marigayin ya shafe shekaru 41 da watanni 6 a kan karagar mulkin ƙasar, kafin rai yayi halin sa. A yanzu kuma ɗansa mai suna Ali bin Bongo shine shugaban ƙasar, bayan nasarar daya samu a zaɓen da aka gudanar.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Zainab Mohammed