Wane sirri ne yake tattare da ƙwayar iri | Amsoshin takardunku | DW | 11.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Wane sirri ne yake tattare da ƙwayar iri

Bayani akan sirrin da ke ƙunshe a cikin ƙwayar iri

default

Ƙwayoyin iri a tafin hannu

Masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, sannunmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Amsoshin takardunku, shirin da a kowane mako yake amsa wasu daga cikin tambayoyin da kuka aiko mana.

Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun Malama Hindatu Hamza daga Jamhuriyar Nijer; Malamar tana so ne a sanar da ita irin sirrin dake tattare da ƙwayar iri da har ya sa take iya fitar da tsiro daga jikinta.

Amsa: Ƙwayar iri dai ɗaya ce daga cikin ɗimbin halittun da Allah ya halitta a doron ƙasa. Shi Allah mahalicci shi kaɗai ne ya barwa kansa sanin iyakacin sirrin dake tattare da ƙwayar iri, to amma kasancewar dukkan wata halitta da Allah ya halitta a doron ƙasa bai halicce ta a banza ba, shi ya sa ɗan Adam yake yin nazari akan halittun Allah domin ya gano iya abin da zai iya ganowa na ilimummukan dake tattare da waɗannan halittu domin tunani ga masu hankali.

Shin ko ɗan Adam ya taɓa yin cikakken tunani a game da ‘ya‘yan itatuwan lambu, ko kuma kyawawan furannin da muke gani a daji ko kuma kyawawan bishiyoyin da suke kewaye da mu?

Shin ko ɗan Adam ya taɓa tunani ko kuma sanin yadda shuka take samuwa da kuma mataki-mataki da take bi na girma kafin ta zama cikakkiyar bishiya?

Ko kuma kawai ɗan Adam yana tunani ne na cewar tsirrai dai kawai wasu halittune da suka samu domin su bayar da sha’awa amma ba su da wata ma’ana ga rayuwar ɗan Adam saboda haka ba ka damu ace akwai su ko babu su ba.

To in dai tunanin ɗan Adam ya kasance haka to babu shakka Mutum yana yaudarar kansa ne, domin kuwa saboda tsirrai ne aka samu daidaituwar iskar da muke shaƙa kuma da taimakonsu ne gubar da take cikin iskar da muke shaƙa bata cutar da mu. Haka zalika da taimakon tsirrai ne muke samun daidaituwar yanayi, babu tsananin zafi kuma babu tsananin sanyi. Wato ma’ana dai tsirrai suna taka muhimmiyar rawa a rayuwar ɗan Adam domin shi ɗan Adam ɗin ya samu sukuni na samun ingantacciyar rayuwa a doron ƙasa.

Kuma fa ba wai waɗannan ne kaɗai amfanin tsirrai ba, a’a hatta magunguna da muke samu kodai na gargajiya ko kuma na Bature duk ana samun su ne daga jikin tsirrai.

Kowa dai yasan yadda ƙwayar iri take, kuma kowa yasan cewa tsirrai suna samuwa ne daga iri. Amma kaɗan ne daga cikin Mutane suke mamaki da al’ajabi akan ko ta yaya ake samun tsirrai daban-daban suke fitowa su girma daga jikin wani ɗan ƙankanin abu, kusan ma ace a zahiri abu mara rai. Har ila yau kuma Mutane kaɗan ne suke tambayar kansu ko yaya ƙwayar iri ta ƙunshi bayanan da suke tabbatar da kamanni da kuma siffofi na tsiron da zai fita daga jikinta. Shin ta yaya ma aka yi ‘ya’yan itatuwa suke da ɗanɗano daban-daban, wasu masu tsananin zaƙi da daɗi amma ace wai duk wannan ya fito ne daga wani ɗan ƙanƙanin abu kuma busasshe.

Shin a haƙiƙanin gaskiya kuwa ƙwayar iri ce take samar da tsiro a siffar da yake kasancewa kuma ta wadata shi da ‘ya’ya?

Shin ƙwayar iri ce take tsara yadda siffa da kuma kalar ‘ya’yan itace da fulawa ya kamata su kasance? Ko kuma dama dai ƙwayar iri tana ɗauke ne da duk bayanan kamanni da siffofi da komai da komai na tsiro a cikin wata mahaifa tata.

To in dai Mutane za su ringa baiwa tambayoyi irin waɗannan wani tunani da nazari na musamman to za su fara mamaki akan ta yaya ƙwayar iri tasan yaya za ta haifi bishiya?

Ta yaya wani ɗan mitsitsin abu zai san ko wacce irin siffa da kuma kama na bishiyar da zai haifa ya kamata ya kasance? Kuma wannan tambaya tana da matuƙar muhimmancin gaske, saboda ba wai kawai taron katakwaye ne suke tsirowa daga jikin ƙwayar iri ba. Misali; mun san cewa bishiyar mangwaro kamar sauran bishiyoyi tana tsirowa ne daga wani ɗan-ƙwallo na iri da aka shuka a ƙasa. To amma ta wasu hanyoyi da ba a san su ba; ana nan wani lokaci wannan ɗan ƙwallon sai a ga ya haifar da wata katuwar Bishiya mai tsawon gaske da kuma girma. Kuma nagartattun ‘ya’yan mangwaron wannan bishiya suna da tsaftataccen jiki , wani lokaci ma har sheƙi suke yi, sannan kuma ga ƙamshi mai daɗi da kuma wani ruwa mai zaƙi da daɗin ɗanɗano.

Kusan dai ko wacce ƙwayar iri idan an shuka ta tana haifar da wata halitta ta tsiro mai cike da kamala, wanda ko da cikakken Mutum mai basira kuma gwani wajen zane yana samun wahala ƙwarai da gaske wajen zana cikakkiyar siffa ta bishiya, ballantana kuma idan aka ce sai ya zana har da dukkanin saiwoyin bishiyar da resunanta. To amma sai ga shi ƙwayar iri tana samar da irin wannan kasaitacciyar bishiya haɗe da siffofi da kamanni da ‘ya’ya da duk abinda ta ƙunsa na rayuwarta.

Duk da cewa muna cewa ƙwayar iri ta haifa, amma ya kamata mu tunawa kammu cewa ita fa ƙwayar irin nan ba ta da wata zuciya abar dogaro, haka zalika bata da wani tunani ko buri. Kuma dama dai abu ne mawuyaci ace ƙwayar iri ce akan kanta ta, ta samarwa da kanta irin wannan aiki. Domin idan aka ce iri ne da kansa ya samarwa da kansa irin wannan aiki, to kenan hakan yana nufin kwayar iri tana da wani katafaren ilimi wanda yake ɗauke da hikima fiye ma da ta ɗan Adam.

Saboda haka bayani anan shi ne cewar, a tattare da kwayar iri an ƙunsa wani ƙasaitaccen ilimi haɗe da wata ƙasaitacciyar hikima wanda yake ko shakka babu ba na ita kanta ƙwayar iri ba ne, saboda haka dole ne ya kasance cewar wannan katafaren ilimi an ƙunsa shi ne a cikin ƙwayar iri ta wata hanya daban.

To idan aka yi tunani mai zurfi a nan za a kai ga yanke hukunci cewa, a gaskiya batun ƙwayar iri busasshiya kuma a zahiri maras rai, ba za ta iya yin komai ba a karan kanta. Wannan ilimi an dasa shi ne a jikin ƙwayar iri daga wani ƙasaitaccen iko da ba shi da kishiya, kuma wannan ƙarfin iko ba na kowa ba ne sai dai a ce na Allah ne mahaliccin komai kuma wanda ya san komai. Shi alkhaliƙu ya halicci ƙwayar iri ne a tattare da ilimi da kuma tsarin da zai mayar da wannan iri zuwa tsiro. Don haka duk wata ƙwayar iri da aka binne a ƙasa to tana lulluɓe ne cikin ilimin Allah ta’ala wanda ya ke sa tsiro ya fito kuma ya girma a kan cikakkiyar siffar da Allah ya ƙaddara masa.