Wane shugaban ƙasa ne yake samun albashi mafi yawa a duniya | Amsoshin takardunku | DW | 25.02.2008
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Wane shugaban ƙasa ne yake samun albashi mafi yawa a duniya

Bayani game da shugaban ƙasar da ya fi dukkanin shugabannin ƙasashen duniya yawan albashi.

default

Firaministan Singapor Lee Hsien Loong a dama, Ministan kuɗi na Jamus Peer Steinbrueck a hagu

Masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkanmu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Amsoshin takardunku, shirin da a kowane mako yake amsa wasu daga cikin tambayoyin da kuka aiko mana.

Tambaya: Tambayarmu ta wannan makon ta fito ne daga hannun Malam Yahuza Sabi'u Sarki, daga birnin Yawunde dake ƙasar Kamaru. Malamin cewa ya yi; Filin Amsoshin takardunku; ku sanar da ni, tsakanin shugabanin ƙasashen duniya, wanene ya fi samun albashi mafi yawa?

Amsa: To kafin muje kai tsaye ga tambayar Malamin za mu so ya sani cewar tsakanin masu riƙe da muƙamai na siyasa a duniya, ‘yan Siyasar ƙasar Singapor, su ne suka fi samun albashi mafi tsoka tsakanin masu muƙamai na siyasa a ƙasashen duniya. Sannan, idan za mu je kaitsaye ga tambayar Malam Yahuza Sabi'u, sai mu ce Firaministan ƙasar Singapor, shi ya fi samun albashi mafi tsoka tsakanin shugabanni na ƙasashen duniya. Kamar yadda kanfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito ranar 13-ga watan Dizamba- 2008, ya nunar cewa, a kowace shekara Firaminista Lee Hsien Loong, kan karɓi kuɗin albashi da ya kai Dallar Singapor milyan 3,760,000. Wanda hakan ya yi dai-dai da Dallar Amirka milyan 2,600,000.

Wannan albashi na Firaministan Singapor, in dan abin ace za'a kwatanta shi ne da albashin wasu shugabanin duniya, za'a iya cewa, kuɗin albashin Firaministan na Singapor ya ruɓanya na shugaban Amirka George Bush, har sau shida. Ya ruɓanya albashin Firaministan Birtaniya Gordon Brown har sau bakwai, ya ruɓanya na shugaban ƙasar Faransa har sau bakwai da rabi, ya ruɓanya har sau takwas kuɗin albashin shekara na shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, sa'anan ya ruɓanya har sau 32, albashin shekara na shugaban ƙasar Rasha, Vladimir Putin.

To wata ƙila mai tambayar zai so ya san ko nawa ne shugaban na Amirka ke ɗauka a shekara a matsayin albashi ? To amsar a nan ita ce shugaba Bush kan lale kuɗi ne daya kai Dallar Amirka dubu 400,0000 da wasu ‘yan matsabbai, sannan mataimakinsa Dick Cheney kan sami kuɗi Dallar Amirka dubu 200,000 shi ma da wasu ‘yan canji a sama. Shi kuwa Firaminista Gordon Brown na Birtaniya, albashinsa a shekara ya kai Dallar Amirka dubu 375,000. Sai kuma shugaba Nicolas Sarkozy na faransa, wanda ke ɗaukan albashin Dalla dubu 346,000. Ita kuwa shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel kan sami Dalla dubu 318,000 ne a matsayin albashinta a kowace shekara. Yayin da kuma shugaban Rasha Vladimir Putin, ke samun albashin Dalla dubu 81,000 duk shekara.

Idan za mu taɓo batun masu riƙe da muƙamai na siyasa kuwa a duniya duk da hakan ƙasar Singapor, ce ke bada kuɗi mafi tsoka ga ‘yan Majalisar dokokinta a matsayin kuɗin alawus. Domin kuwa sukan sami abin da ya kai Dala ta Singapor dubu 225,000 a matsayin alawus, kowace shekara.

 • Kwanan wata 25.02.2008
 • Mawallafi Bashir, Abba
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/DD89
 • Kwanan wata 25.02.2008
 • Mawallafi Bashir, Abba
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/DD89