Wane shugaban ƙasa ne ya fi daɗewa akan karagar mulki a Nahiyar Afirka | Amsoshin takardunku | DW | 09.06.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Wane shugaban ƙasa ne ya fi daɗewa akan karagar mulki a Nahiyar Afirka

Taƙaitaccen tarihin shugaban ƙasa mafi daɗewa akan karagar mulki a Nahiyar Afirka

default

Shugaba Omar Bongo na Gabon

Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun Mathew Garba daga Maiduguri a tarayyar Najeriya, wanda ya ce,

tambaya ta ita ce; A Nahiyar Afirka, wane shugaban ƙasa ne ya fi daɗewa akan karagar mulki a halin yanzu?


Amsa: A halin yanzu, shugaban da ya fi daɗewa a kan karagar mulki a Nahiyar Afirka da ma duniya baki ɗaya, shi ne El hadj Omar Bongo Ondimba na ƙasar Gabon. An dai haife shi ne a ranar 30 ga watan Disamba a shekara ta 1935, kuma ya zama shugaban ƙasa a shekara ta 1967, a lokacin ya na da shekaru 31, kuma a wancan lokaci, shi ne shugaba mafi ƙarancin shekaru a duniya. A yanzu ya na da shekaru 41 akan kujerar mulki.


Ainihin sunan sa dai shi ne Albert Omar Bongo Ondimba, amma da ya rungumi Addinin Musulunci a shekara ta 1973, sai ya canja sunan sa zuwa El hadj Omar. An haife shi ne a Lewai, wani gari ne dake kudu maso gabashin Gabon, kusa da iyaka da jamhuriyar Kongo. Saboda irin ƙoƙarin da ya yi na haɓaka garin na Lewai, ya sa jama'ar garin suka canja wa garin suna zuwa Bongoville, wato suka sa ma garin sunan shugaban ƙasar kenan.


A shekara ta 2003, aka canja kundin tsarin mulkin ƙasar don a kauda duk wani abu da zai kawo cikas ga wa'adin da shugaba zai iya yi akan karagar mulki. Hakan ya sa masu sukar gwamnatin Bongo suka zarge shi da niyyar yin shugabanci na har abada.

A ranar ɗaya ga watan Oktoba, Shugaban ƙasar ya sanar da tsayawa takara a zaben shekara ta 2005, sannan aka sanar da cewa za a gudanar da zaɓen a ranar 27 ga watan Nuwamba. Sakamakon da ya fito bayan kammala zaɓen, ya nuna cewa Bongo ya sami nasara da kimanin kashi 79 na ƙuri'u. Wanda ya sa aka rantsar da shi a ranar 19 ga watan Janairu shekara ta 2006, na wani wa'adin mulki na tsawon shekaru bakwai.


Yanzu dai shugaban ƙasar ta Gabon ya tasamma shekaru 60 da haihuwa, kuma bai nuna wata alama ta sauka daga shugabanci ba, musamman ma tun da an canja tsarin mulkin ƙasar, wanda ya ba shugaban ƙasar damar yin mulki na shekaru bakwai har sau biyu. Saboda haka, yana iya kasancewa akan karagar mulki har zuwa shekara ta 2012.


Shugaba Bongo ya yi suna a duniya saboda ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya a wasu ƙasashe na Afirka, kamar a ƙasashen dake tsakiyar Afirka, Kongo-Brazzaville, Burundi da Jamhuriyar Kongo.


Sannan a ƙasarsa ta Gabon, ya yi suna saboda kuzarinsa da kuma nuna gaskiya a sha'anin mulki, musamman ma da yake an samu zaman lafiya a shugabancinsa. Kuma babban sirrinsa shi ne kula da ci-gaban al'amuran matasa.