1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wane mutum ne ya ƙirƙiro cingam

Bashir, AbbaJune 2, 2008

Taƙaitaccen tarihin mutumin da ya ƙirƙiro da cingam a duniya

https://p.dw.com/p/EBQW
Wata budurwa tana hura cingamHoto: APTN

Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga Hannun Malama Ramatu Jafaru daga Jamhuriyar Benin, wadda tace, don Allah ina so ku sanar da ni  asalin yadda aka samo cingam, kuma ku bani tarihin mutumin da ya ƙirƙiri cingam ɗin.


Amsa: Shi dai cingam ya samo asali ne, tun kusan shekara ta 1860,inda wani mai suna Thomas Adams ya fara tunanin yin cingam kuma ya yi nasarar haka a 1871.


koda yake akwai wasiwasi akan cewa shi ne ya fara yin cingam, duk da haka, shi ne ya fara ƙirƙiro na'urar da aka fara amfani da ita don yin cingam. Shi dai Thomas Adams, wanda ya rayu tsakanin 1818 zuwa 1905, ya fara amfani da wani sinadari ne mai gam, da ake samu daga wata itaciya a kasar Mexico, da nufin  yin wasu abubuwa kamar su tayar keke, takalman ruwa da abubuwan wasan yara, amma hakan bai yiwu ba.


Yusuf: Wata rana a 1869, sai ya jefa wannan sinadarin a cikin bakin sa ya fara taunawa, da yin haka kuwa, sai ya ji sinadarin yana da daɗi a baka. Da ya ji yana da dadi, sai tunanin ya ƙara ma sinadarin gallura da kayan ƙanshi ya shiga zuciyarsa, kuma sai ya yi hakan.


To ba da daɗewa ba kuwa, sai ya buɗe kamfani na farko a duniya na yin cingam, kuma a 1871, aka fara sai da cingam mai suna Adams New York Gum, a shaguna da wurare da dama a Amirka


koda yake tun farko an fara sarrafa cingam ne daga sinadarin da ake samu daga wannan itaciyar da muka ambata a baya, yanzu saboda bukatuwa na tattalin arziki da kuma inganci, akan yi amfani ne da roba a wasu wuraren don yin cingam, sai dai kasar Japan, wadda har yanzu tana amfani ne da sinadarin na asali.