Wane mutum ne aka fi yawan tsarewa a kurkuku | Amsoshin takardunku | DW | 17.09.2007
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Wane mutum ne aka fi yawan tsarewa a kurkuku

Bayani game da Mutumin da ya fi kowa yawan shiga kurkuku a Duniya

wasu yan-fursuna a gidan yari

wasu yan-fursuna a gidan yari

Masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, sannunmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Amsoshin takardunku, shirin da a kowane mako yake amsa wasu daga cikin tambayoyin da kuka aiko mana.

Abdullahi: Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun Malam Yunusa Bilal daga Jihar kano a tarayyar Najeriya. Malamin cewa yayi; Don Allah ina so ku gano min; shin wane mutum aka fi yawan kullewa a kurkuku a wannan Diniya tamu?

Bashir: To kamar dai yanda kundin tattara bayanai a Duniyar-Yanar gizo ya nunar, wato Wikipedia. Wani mutum da ake kira da suna Mr Henry Earl Shine mutumin da aka fi yawan tsarewa a gidan yari, kasancewar bayanai sun nuna cewa, ya zuwa watan Yuli na wannan shekara da muke ciki an tsare Mr Earl a Gidan yari har sau 949. Bayanai da aka tattara daban daban wadanda suka hada har da hira da shi wannan mutumin mai dabi’ar aikata laifi ko da yaushe, sun nunar da cewa, Mutumin ya kasance bashi da gidan kwana kuma ba shi da aikin yi tun cikin shekara 1969, sabodahaka ya karar da kusan dukkanin rayuwarsa a gidan yari kuma badon komai ba sai don yawan shaye-shaye a bainar jama’a.

An dai haifi Mr. Henry Earl ranar 24 oktoba 1949, a garin Lexington da ke jihar Kentucky a kasar Amurka, kuma ya kasance mutum ne Dan-tasha, wanda bashi da gida kuma bashi da Dangi. Mr Earl ya zama sananne ne ta hanyar Duniya –yanar gizo wato internet, sakamakon wani yunkuri da gidan yarin garinsu ya yi na watsa hatunan masu laifi wadanda aka taba kullewa a gidan yarin, na Da da na Yanzu. Inda suna da kuma hoton Earl ya fi na kowanne dan fursuna yawa.

Sakamakon haka yasa Mr. Earl ya dauki hankalin mutane in da aka fara binciken ko akwai wani wanda ya fi shi yawan shiga gidan yari a wannan Duniya?wanda daga karshe dai ba’a samu wanda ya ke gaba da shi a wannan mukami ba.

Bayanai dai sun nuna cewa, ya zuwa yanzu Mr. EARL an yanke masa hukuncin dauri har sau 949 , kuma idan aka hada kwanakin da ya yi a gidan yari a lokuta daban-daban za’a samu cewar ya shafe kwanaki 3806 a gidan wakafi.

 • Kwanan wata 17.09.2007
 • Mawallafi Abba Bashir
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvUi
 • Kwanan wata 17.09.2007
 • Mawallafi Abba Bashir
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvUi