1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wane gini ne mafi tsawo a duniya

Bashir, AbbaMarch 30, 2008

Bayani game da tarihin dogwayen gine-gine

https://p.dw.com/p/DXVc
Burj Dubai shi ne gini mafi tsawo a duniyaHoto: EMAAR

Masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Amsoshin takardunku, shirin da a kowane mako yake amsa wasu daga cikin tambayoyin da kuka aiko mana.

Tambaya: Ina son ku sanar da ni asalin tarihin dogwayen gine-gine . kuma ina so na san gini mafi tsawo a duniya a yau da kuma a nan gaba. Wannan ita ce tambayar da muka samu daga hannun Malam Ado Inuwa daga Makurdi a Jihar Benue ta tarayyar Najeriya.

Amsa: To tarihin dogwayen gine-gine dai za a iya bin diddiginsa tun shekaru ɗaruruwa ko ma ace dubbai da suka wuce, lokacin da maƙera da kuma maginan asali suka fara yin ƙoƙarin gina dogwayen gine-gine Mahadi ka ture. Kama dai daga dalar giza ta ƙasar Misra, har zuwa ƙasaitaccen ginin hasumiyar birnin Dubai wanda yanzu haka ake tsaka da gininsa.

Tun shekaru da dama da suka gabata lokacin da aka fara samun ci gaba a ɓangaren fasahar gine-gine, masana ilimin zanen gine-gine suka riƙa zana da kuma ƙirƙirar samfuri daban-daban na dogwayen gine-gine, kama dai daga ofisoshi na ma'aikatu yadda za su ɗauki ma'aikatu da dama, har ya zuwa hotel-hotel da Asibitoci da kuma Gidajen Tarihi. Har ila yau kuma sakamakon juyin zamani da yanayin muhalli da kuma buƙatun al'umma ya sa tsarin dogwayen gine-gine yake ƙara zama ruwan dare gama duniya.

To idan kuwa ana batun gini mafi tsawo a duniya sai a ce, ginin hasumiyar birnin Dubai da ke haɗaɗɗiyar daular larabawa, shi ne gini ma fi tsawo yanzu haka a duniya, kuma kasancewar ba a kammala shi ba tukuna, ana ƙara bayyana shi da cewa shi ne gini ma fi tsawo da aka sani zai tabbata a nan gaba. In da yanzu haka shi wannan gini ya kai hawa 145 kamar dai yadda maginan suka bayyana. Kuma in ban da shi, ba bu wani gini a doron duniyar nan da ya kai hawa 145.

An dai fara gina wannan hasumiya ta birnin dubai a ranar 21ga watan Satumba, 2004. Kuma ana sa ran kammala shi a shekara ta 2009. Idan aka kammala shi, ginin zai kasance yana da sama da hawa 160.