1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Wane abu ne a cikin giya ke haifar da maye

Taƙaitaccen bayani game da sinadarin cikin giya wanda ya ke haifar da maye

default

Wani saurayi riƙe da kwalbar giya yana kirari

Tambaya:Wane abu ne a jikin giya ke haifar da maye, kuma me ya sa wanda ya sha giya ko da yana cikin hayyacinsa sai ya riƙa yin wasu abubuwa ko dai na batsa ko na rashin kunya da dai sauransu? Wannan ita ce tambayar da muka samu daga hannun malama Harira Abdullahi daga birnin Yamai na Jamhuriyar Nijer.

Bashir: To dafarko dai malama Harira, binciken da muka yi ya nunar da cewa, ita dai giya ta kasance annoba ga rayuwar bil'adama tun shekaru aru-aru da suka wuce. Kuma ta ci gaba da haifar da asarar rayukan al'umma, kuma ta haifar da mummunan lahani ga rayuwar miliyoyin mutane a wannan duniya. An hakikance cewa, giya ita ce ummul abaisin matsaloli da dama da ke addabar al'umma. Ƙididdiga ta nunar da cewa yawan yaduwar fitintinu da ciwukan ƙwaƙwalwa da kuma hargitsa rayuwar iyali duk na daga cikin abubuwan da ke faruwa saboda tasirin da giya take da shi ga rayuwar bil'adama.

Yusuf: Shin me addinai suka ce game da giya?

Bashir: To babu shakka kusan dukkan manayan addinan wannan duniya sun yi umarni ga mabiyansu da su ƙauracewa shan giya. Misali a littafin Baibil a surar Proverbs wato sura ta 20:1 da kuma surar Ephesians wato sura 5:18, duk sun gargadi mutum da cewa ya nisanci giya. Haka zalika a cikin Alkur'ani a wurare da dama Allah ya yi umarni da a nisanci giya, misali a suratul ma'ida wato sura ta 5:90

Yusuf: To wane dalili ne ya sa mashayin giya a wani lokaci yake aikata ayyukan assha?

Bashir: Dalili shi ne, wato a cikin ƙwaƙwalwar ɗan-Adam, akwai wata halitta da take sa mutum jin kunya, take sa mutum ƙoƙarin aikata alheri da kuma gujewa mummunan aiki. Misali ita ce take hana mutum yin ashare-ashare, ko fitar da tsiraici a bainar jama'a da dai sauransu.To amma yayin da mutum ya sha giya sai ta tafi kai tsaye wajen wannan halittar da ke cikin ƙwaƙwalwa da take hana mutum aikata aikin assha, sai giyar ta birkita saitin wannan halitta, shi ya sa sai mutum ya shiga yin wasu halaye nan take waɗanda kwata-kwata sun saɓa da halayensa. Misali ashare-ashare, rashin fahimtar kuskure idan ma ya yi, rashin girmama na gaba musamman iyaye, yin bawali ajikinsa, ana tafiya ana layi ana kauce hanya da dai sauran ɗabi'un da ba daɗin ji ba kyan gani.

Yusuf: Ko yaya giya ta taimaka wajen haifar da laifuffuka irin su fyaɗe kisan kai da dai sauransu?

Bashir: To Kamar yadda wata ƙididdiga ta hukumar shari'a ta ƙasar Amirka ta nunar, ta bayyana cewa a 1996 a hukumance a ƙasar Amirka a kowacce ranar Allah an yiwa mata 2,713 fyaɗe. Kuma wannan ƙididdiga ta nuna cewa mafiya yawan masu fyaɗen sun aika shi ne sakamakon giya da suka sha. Kuma haka abin yake ga cin zarafi. Har ila yau ƙididdigar ta nuna cewa kashi 8 daga cikin Amerikawa suna zina da muharramansu, wato ko dai ‘ya'yansu ko ƙannensu ko iyayensu. Kuma a mafi yawan lokuta akan tarar cewa ɗaya ko duka waɗanda abin ya shafa suna cikin mayen giya. Baya ga haka kuma wani Babban abin da ake danganta yaɗuwar cutar AIDS ad shi, ita ce giya.

Yusuf: Wasu sukan ce ai ba kowa ne yake maye idan ya sha giya ba?

Bashir: Babu shakka, to amma koda ace sau ɗaya a tak mashayin giya yai maye a rayuwarsa, sakamakon haka ya aikata fyaɗe ko zina da muharraminsa, to ko shakka babu ga cikakken mutum mai hankali ko da ya yi danasanin abin da ya aikata, to wanna illa za ta ci gaba da damunsa har iyakacin rayuwarsa. Sannan kuma idan aka koma batun cututtuka na zamani, mun sha yin shirye-shirye da likitoci akan cututtukan da giya ke haifarwa, waɗanda suka haɗa da cutar hanta da cutar daji, ga sunan dai barkatai.

Yusuf: To a ƙarshe mece ce shawara:

Bashir: To shawara ita ce ko da likito ci a yanzu sun tabbatar da cewa, shan giya fa cuta ne ba wai sabo ba ne. In da kuma masharhanta akan batun giya suka bayyana cewa;

Na farko dai, in dai an yarda cewa shan giya cuta ne, hakan na nufin kenan;

Giya ita kaɗai ce cutar da ake sayarwa da mutane a cikinkwalba.

Ita kaɗai ce cutar da ake tallanta a kafafan yaɗa labarai, jaridu, mujallu radio, da talabijin.

Ita kaɗai ce cutar da take da lasisin watsuwa tsakanin al'umma

Ita kaɗai ce cutar da take samar da kuɗin shiga ga hukumomi.

Ita kaɗai ce cutar da take haifar da munanan haɗurra a tituna

Ita kaɗai ce cutar da take wargatsa rayuwar iyali tare da ƙara haifar da fitintinu tsakanin jama'a.

Ita kaɗai ce cutar da ba kwayoyin cuta ne ke haifar da ita ba.

Saboda haka giya dai ƙazanta ce daga ƙazantar sheɗan, don haka sai a guje ta.