Wanda aka Haifa Bayahude ne kawai ke shiga addinin Yahudanci? | Amsoshin takardunku | DW | 06.05.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Wanda aka Haifa Bayahude ne kawai ke shiga addinin Yahudanci?

A Addinin Yahudawa wanda mahaifiyar sace bayahudiya yake zama bayahude koda kuwa mahaifinsa ba bayahude bane.

default

Wasu Limaman Yahudawa

Yahudanci dai ɗaya ne daga cikin addinai na ahalil kitabi wato yahudanci da kuma Kiristanci. Kuma addinin musulunci yayi batu game da wannan addini kamar yadda kuma Annabin daya aiko masu shine annabi Musa (AS). Kuma sun samo asali ne daga ɗaya daga cikin 'ya'yan Annabi Ibrahim (AS) wato Annabi Ishak. Sannan kuma akwai Annabawa da yawa a cikin su kama daga Annabi Yakub da 'ya'yansa irinsu Annabi Yusuf da Musa da Haroun (AS).

A addinin Yahudawa wanda mahaifiyar sace bayahudiya yake zama bayahude koda kuwa mahaifinsa ba Bayahude bane. Game da rayuwa kuwa, yahudawa na gudanar da wasu al'adu da suka sha banban dana musulunchi. Misali shine inda Ɗanfari shine zai gaji mahaifinsa koda kuwa yana da ƙanne shine zai samu mafi yawa daga cikin kayan gadon saɓanin a ɓangaren addinin musulunci.

Haka kuma babu banbanci tsakanin Ɗan da za'a Haifa a rariya da kuma na aure, a lokaci guda kuma suna cewa mata idan tayi aure tana ƙarƙashin mijinta ɗari bisa ɗari sai abinda yayi da ita. Koda yake a yanzu mata suna da 'yanci a ƙarƙashin sabbin dokokin na Isra'ila. Kuma duk mutumin daya haura shekaru 20 musanman tsakanin masu tsautsaurar ra'ayi baiyi aure ba, to lallai wannan na cikin hatsarin tsinuwa na iya faɗo masa. Kana kuma sun yarda ayi aure fiye da biyu musanman tsakanin wa'yanda aka kira Rabbaniyun sunce kar a wuce huɗu, wasu kuma sunce sai inda ƙarfin mutun ya tsaya.

A cikin masu tsautsaurar ra'ayi musanman wa'yanda ke ganin ba ruwan su da addini sun dage cewar ai yahudanci ba komai bane illa jinsi, saboda haka batun wani ma ya shiga addinin wanda ba Bayahude bane baima taso ba. To sai dai wasu kuma suna ganin duk wanda yakasance Bayahude ne bazai taɓa fita ba.

Sai dai dokokin Israilan a yanzu sunce idan dai da yardan ka kaso fita ba tare da ƙuntatawa ba, mutun na iya ficewa.

Amma kuma suma sun yarda cewar shiga wannan addinin nasu abune da zasu iya amincewa dashi matukar dai mutum ya nuna kyaukyauwar niyya kuma ya gamsar da malaman yahudawan wato (Hahamawa) da cewar da kyaukyauwar niyya yake son shiga addinin bada wasa ba. A cewar su akwai mutane da dama dake son shiga addinin nasu, su kuma ba zasu hana su shiga ba, muddin akwai manufa ta gari.

Yanzu hakama dai shugabanin yahudawan na fafutukan shawo kan gwamnatin Israila na sassauta wannan Doka ta yarda za'a bari duk wanda keson shiga addinin musanman idan yana da maiko ya samu sukunin yin hakan. Yahudawa dai sun daɗe a ƙasashen larabawa dana Musulmi suna rayuwa ba tare da wata matsala ba. Amma kafa Israila a shekarar 1947 shiya fara ɗiga ɗanba na raba gari kuma da yawa daga cikin su sun koma ƙasar tasu ta Israila. Amma kuma ko'a yanzu akwai ɗakunan ibada na Yahudawa daban-daban kamar ƙasar Masar da Yamen da Tunisiya da dai sauran ƙasashen na Larabawa. Kuma irin wa'yannan guraren ibada na samun kariya daga hukumomi ganin irin baƙin jinin da Yahudawan kedashi a tsakanin Larabawa sakamakon matsalar su da Palasɗinawa.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Ahmad Tijjani Lawal