1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wakilin Mdd ya isa kasar Burma

September 29, 2007
https://p.dw.com/p/Bu9t

Wakilin musanman na Mdd, Farfesa Ibrahim Gambari ya isa kasar Burma. Ana sa ran Mr Gambari zai tattauna ne da mahukuntan kasar, don samo bakin zaren warware rikice rikicen siyasa da kasar ke fama dashi.Har ilya yau Ibrahim Gambari zai kuma gana da shugabar adawa ta kasar, wato San Su Kyi, da a yanza haka ke tsare a matsayin daurin talala. Kafafen yada labarai dai sun rawaito faraministan Malaysia, Abdullah Ahmad Badawi na jaddada muhimmancin zuwan Mr Gambari izuwa kasar ta Burma:

Abdullah Ahmad Badawi yace, Malaysia na goyon bayan wannan mataki na Mdd, kuma muna kira ga mahukuntan Burma dasu bawa Mr Gambari goyon bayan daya dace,don cimma burin daya kai shi kasar a matsayin wakilin Mdd.

Hankalin duniya dai ya karkata kann kasar ta Burma ne, bayan da sojoji a kasar suka bude wuta kan masu zanga zangar adawa da gwamnatin kasar. Hakan dai ya haifar da rasuwar fararen hula 13 da kuma jikkatar wasu da dama. Rahotanni sun kuma shaidar da cewa yan sanda sun kuma yi awon gaba da wasu daruruwan masu zanga zangar. A yanzu haka dai kasashe da kungiyoyi, na ci gaba da matsawa gwamnatin mulkin soji ta kasar lamba data saurari koke koken masu zanga zangar.