Wakilin Mdd na musanman ya kammala aikin sa a Burma | Labarai | DW | 02.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wakilin Mdd na musanman ya kammala aikin sa a Burma

Wakilin Mdd na musanman a Burma, yayi ganawa zagaye na biyu da shugabar adawar nan San Suu Kyi.Tattaunawar ta Ibrahim Gambari da San Suu Kyi ta mayar da hankali ne kann yadda za´a shawo kann rikicin siyasar kasar.Kafin dai barin sa Burma, Mr Gambari ya kuma gana da shugaban mulkin sojin kasar, janar Than Shwe.A yanzu haka dai Mr Gambari ya bar kasar izuwa Singapore, kafin komawar sa gida.Hankalin duniya dai ya karkata kann Burma ne, bayan da sojin kasar suka bude wuta kann masu zanga zanga dake adawa da gwamnati. A yanzu haka dai rahotanni sun shaidar da rasuwar mutane a kalla 200, sakamakon rikice rikice na siyasa a kasar.