Kungiyon da za su wakilci Jamus a kakar badi
May 16, 2018Talla
A yayin da Kungiyoyin Bayer Leverkusen da Leipzig suka samu tikitin buga kai tsaye gasar cin kofin hukumar kwallon kafa ta Turai ta UEFA wato Europa Lig. Akwai sauran tikiti daya na shiga gasar Europa Lig bayan buga wasan ketara siradi na Play off wanda kungiyar za ta koma ko dai a hannun Stuttgart da ke a matsayin ta bakwai ko kuma Frankfurt ta takwas idan har ta lashe kofin kasar Jamus a wasan da za ta buga da Bayern Munich a ranar Asabar.