Wajibi ne Jamus ta sake nazarin dokokinta game da manema mafakar siyasa | Siyasa | DW | 28.04.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Wajibi ne Jamus ta sake nazarin dokokinta game da manema mafakar siyasa

Kantoman MDD akan al'amuran 'yan gudun hijira Ruud Lubbers yayi kira ga Jamus da ta dauki nagartattun matakai domin ba da kariya ga manema mafakar siyasa da suka hada har da mutanen da kan yi kaura daga kasashensu sakamakon kabilanci ko wariyar jinsi ko rigingimu na addini ko kuma tabarbarewar al'amuran tsaro

Kantoman MDD akan al'amuran 'yan gudun hijira Ruud Lubbers

Kantoman MDD akan al'amuran 'yan gudun hijira Ruud Lubbers

Kantoman MDD akan al’amuran ‚yan gudun hijirar Ruud Lubbers, wanda ya gabatar da kiran nasa a Berlin ga kwamitin nazarin sabuwar dokar kaka-gida a Jamus, ya gana da shugaban kasa Johannes Rau da kuma ministan cikin gida na Jamus Otto Schily. Bisa ga ra’ayinsa wannan sabuwar dokar, wacce ake neman cimma daidaituwa kanta tsakanin gwamnati da ‚yan hamayya tana iya taimakawa wajen kyautata makomar manema mafakar siyasa a nan kasar. Wannan maganar musamman ta shafi babin dokar dake ba da damar kare makomar mutanen da kan kaurace wa kasashensu sakamakon kabilanci ko wariyar jinsi ko rikici na addini. A wannan bangaren dai Jamus na fama da gibi matuka ainun a tsarin dokokinta. A cikin bayanin da ya gabatar Lubbers cewa yayi:

Wajibi ne kuma dokar ta Jamus ta ba da cikakken la’akari ga makomar ‚yan gudun hijirar da kasashensu suka wargaje daidai da abin da yarjejeniyar Geneva akan ‚yan gudun hijira ta tanada.

Kantoman na MDD ya ba da misali da kasashe irinsu Klombiya ko Sudan, wadanda ya ce a halin da ake ciki yanzu ba su da ikon kare lafiyar al’umarsu saboda tabarbarewar tsaro a cikinsu. Ruud Lubbers kazalika yayi kiran kamanta adalci da nuna karimci wajen ma’amalla da ‚yan gudun hijirar, ba ma a Jamus kadai ba har da sauran kasashen Turai. An dai samu raguwar tuttudowar ‚yan gudun hijirar dake kwarara zuwa kasashen Turai domin komawa matsayin da aka fuskanta a cikin shekarun 1980. Kuma a saboda haka ya zama wajibi a rika nuna halin sanin ya kamata wajen tallafar kaddarar da ke rutsawa da ‚yan gudun hijirar da kan yi cincirindo a fafutukar shigowa nahiyar Turai. Wajibi ne kasashen su daina son kai su kuma gabatar da matakan raba nauyi daidai wa daida tsakaninsu dangane da ‚yan gudun hijirar da kan kwarar zuwa kasashe irinsu Poland, wadanda ta kansu ne makauratan kan karasa zuwa ragowar kasashen KTT. Daya matsalar dake ci wa kantoman MDDr akan al'amuran 'yan gudun hijira tuwo a kwarya kuma shi ne ka'idojin da Jamus ta shimfida na mayar da manema mafakar siyasar zuwa kasar da suka bi ta kanta domin karasowa zuwa Jamus, muddin kasar na da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ya ce idan har sauran kasashen kungiyar tarayyar Turai zasu yi koyi da irin wannan mataki to kuwa za a wayi gari ana daukar matakan mayar da ‚yan gudun hijirar zuwa kasashensu kai tsaye. Lubbers yayi godo ga kasashen Turai da su tashi tsaye wajen taimaka wa ‚yan gudun hijirar dake dada yaduwa a sassa dabam-dabam na duniya. Irin wannan mataki shi ne ya taimaka aka cimma nasarar mayar da ‚yan gudun hijirar Afghanistan su kimanin miliyan uku zuwa gida.