WAIWAYE KANN YADDA WASAN KWALLON KAFAR NAHIYAR AFRICA YA KASANCE A SHEKARUN BAYA. | Siyasa | DW | 17.02.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

WAIWAYE KANN YADDA WASAN KWALLON KAFAR NAHIYAR AFRICA YA KASANCE A SHEKARUN BAYA.

To da farko dai hukumar wasan kwallon kafa ta nahiyar ta Africa,wato Caf ta yanke hukuncin shirya wan nan gasar kwallon kafar ce a tsakanin kasashen na Nahiyar africa a kowace shekara biyu.

Kuma,kamar yadda kididdiga ta nunar wasan kwallon kafar na nahiyar ta Africa an fara shine a shekara ta 1957 a can kasar Sudan,wanda a wan nan lokaci kasashe uku ne kawai suka shiga gasar.Kasashen kuwa sun hadar da Masar da Habsha da kuma mai masaukin baki wato Sudan. A wan nan lokaci kasar Masar itace ta samu nasarar daukar kofin,sai kuma kasar Habasha data rufa mata baya a matsayi na biyu,sudan kuma ta kasance a matsayi na uku.
A shekara ta 1959 kuwa kasar masar ita ta dauki bakuncin wasan,wanda a karshe a wan nan karon ma ta dauki kofin kasar sudan kuma ta rufa mata baya. A shekara ta 1962 kuma sai ragamar bakuncin ya koma hannun kasar habasha,wanda itama a wan nan lokaci itace ta samu nasarar daukar kofin bayan ta duke yan wasan kasar Masar.
Kasar Ghana itace ta dauki bakuncin wasan na shekara ta 1963,kuma itace ta zama zakaran gwajin dafi na wan nan lokaci,kana kasar Sudan na rufa mata baya. Har ila yau kasar ta Ghana itace ta zama zakara a gasar da aka karayi a shekara ta 1965 a can kasar Tunisia,wanda a wan nan lokaci Tunisian ta zamo ta biyu.
Kasar Congo kinshasa itace ta dauki kofin zinariyar na wasan kwallon kafar na nahiyar ta Africa a shekara ta 1968.Kasar Ghana kuma na rufa mata baya a matsayi na uku,sai mai masaukin baki wato kasar Habasha data zamo a matsayi na uku. A shekara ta 1970 kasar sudan ta kara daukar nauyin bakuncin wasan,wanda a lokaci ta samu damar zamowa zakara a karo na farko.kasar Ghana kuma na rufa mata baya a matsayi na uku. Kasar Congo Brazzavill itace ta zamo zakara a gasar ta shekara ta 1972 da kasar Kamaru ta dauki bakuncin sa,sai kuma kasar mali data zamo a matsayi na biyu. A shekara ta 1974 kuwa kasar masar ce ta dauki nauyin gasar wasan,kasar Zaire kuwa ta zamo ta daya a inda Zambia take rufa mata baya a matsayi na biyu.
Kasar Morocco itace ta zamo a matsayi na farko a shekara ta 1976,wanda a lokacin kasar Habasha itace ta dauki nauyin shirya wasan.
Akalar daukar nauyin shirin wasan a shekara ta 1978 ta dawo hannun kasar Ghana,a inda a wan nan lokacin ta zamo a matsayi na farko kasar Uganda kuma a matsayi na biyu.
Tarayyar Nigeria itace ta dauki nauyin gasar a shekara ta 1980 kuma a wan nan karon itace ta dauki kofin zinariyar,kana a hannu daya kuma kasar Algeria na rufa mata baya a matsayi na biyu.
A shekara ta 1982 kuwa kasar Libya ce ta dauki nauyin gasar a karo na farko ,wanda a lokacin kasar Ghana ta dauki kofin a karo na hudu bayan da yan wasan kasar dana Libya suka buga ball din daga kai sai mai tsaron gida. A shekara ta 1984 kuwa kasar Ivory Coast ce ta dauki nauyin gasar,wanda a lokacin kasar Kamaru ta dauki kofin a karo na farko,tarayyar Nigeria kuma na rufa mata baya a matsayi na biyu.
Kasar Masar itace ta kara zamowa a matsayi na farko a karo na uku a shekara ta 1986,kana kasar Kamaru na rufa mata baya a matsayi na biyu.
A shekaru na 1988 da 2000 da kuma 2002 kasar kamaru ce ta dauki wan nan kofi na zinariya. A shekara ta 1990 kuwa kasar Algeria itace ta dauki matsayi na farko Nigeria kuma a matsayi na biyu. Sai shekara ta 1992 da kasar Ivory Coast ta dauki Kofin zinariyar a inda tabar kasar ghana a matsayi na biyu. A kuwa shekara ta 1994 Nigeria itace ta kara daukar kofin kasar Zambia kuma na rufa mata baya a matsayi na biyu,kasar Tunisia kuma a wan nan lokaci itace ta dauki bakuncin gasar wasan.
A shekara ta 1996 kuma kasar Africa ta kudu itace ta dauki koFin,kasar Tunisia kuma na rufa mata baya a matsayi na biyu. A shekara ta 1998 kuma kasar Burkina Fasso itace ta dauki nauyin bakuncin wasan.Wanda a lokacin kasar Masar ta zamo zakara.kasar Africa ta kudu kuma na rufa mata baya.
Yanzu kuma a shekara ta 2004 kasar Tunisia ce ta dauki bakuncin wasan,kuma a yau din nan asabar itace ta zamo zakaran gwajin dafi na kwallon kafar na nahiyar ta Africa.Kana a hannu daya kuma kasar Morocco take rufa mata baya a matsayi na uku.