1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Waiwaye kan rikicin Shi'a a Najeriya

December 15, 2016

A tsakanin ranakun 12 zuwa 14 ga watan Disamban na shekarar 2015, sojojin Najeriya sun halaka 'yan Shi'a kusan 340 a garin Zaria da ke arewacin kasar. Sai dai har yanzu babu alamun sulhu tsakanin gwamnati da 'yan Shi'a.

https://p.dw.com/p/2UJLF
Nigeria Demo für die Freilassung von Ibraheem Zakzaky
Hoto: picture alliance/AP Photo/M. Giginyu

Kungiyar kare hakin jama'a ta Human Rights Watch  ta fitar da rahoto tana kira ga gwamnatin Najeriya ta hanzarta sakin shugaban kungiyar ‘yan Shia Ibrahim Zakzaky da ma kawo karshen zargin da take na matsi da murkushe ‘yan Shi'a a kasar.