Waiwaye game da ƙasar Ghana | Siyasa | DW | 06.12.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Waiwaye game da ƙasar Ghana

Zaɓen a ƙasar Ghana don zaɓan wanda zai gaji shugaba Kufuor.

default

Ɗaliban Ghana a dandalin ´yanci dake birnin Accra

A yau Lahadi ake kaɗa ƙuri´a a ƙasar Ghana don zaɓan wanda zai gaji shugaba John Kufuor. A ƙarƙashin Kufuor da kuma magabacinsa wato Jerry John Rawlings Ghana ta tashi daga matsayin wata ƙasa da ta durƙushe zuwa wata kyakkyawar abar koyi a tsakanin ƙasashen Afirka. To sai dai duk da kwanciyar hankalin siyasa da ci-gaban tattalin arziki da da take samu tun a farkon shekarun 1980, har yanzu ƙasar na fama da matsaloli iri daban daban.

Shugaban Ghana na farko kenan wato marigayi Kwame Nkrumah a jawabinsa lokacin da ƙasar ta samu ´yancinta daga turawan Ingila a 1957. Kamar yadda Nkrumah ya nunar a wannan jawabin cewa Ghana ta samu ´yancinta har abada amma shi kanshi bayan shekaru tara aka yi masa juyin mulki. Bayan juyin mulkin farko an ta samun wasu abin da ya jefa ƙasar ta Ghana cikin rashin kwanciyar hankalin siyasa da taɓarɓarewar tattalin arziki har zuwa 1981 lokacin da Jerry Rawlings ya karɓi ragamar mulki karo na biyu.

"Na nunar muku a fili cewa wannan abin da ya faru ya bambamta da sauran juyin mulki. Yanzu mun fara wani juyin juya hali ne wanda zai canza alƙiblar wannan ƙasa. Kuma kamar yadda kuka sani duk abin da ya taɓa hanci dole ido ya yi ruwa."

Duk da mulki irin na kama karya da ya yi, sannu a hankali Rawlings ya aiwatar da kyakyawan canje canjen siyasa da na tattalin arziki a mulkinsa daga shekarar 1981 zuwa 2001. Hakan ya sa Ghana ta tashi daga wata ƙasa da ta durƙushe zuwa abar koyi. Ya ba wa hukumomin ba da lamuni na duniya cikakken haɗin kai sannan ya ƙaddamar da tsarin mulkin demoƙuraɗiyya wanda ya ba da damar kafa jam´iyun siyasa, inda a karshen 1992 aka gudanar da zaɓen da ya zama wani abin tarihi. A shekara ta 2000 Rawlings ya tabbatarwa duniya cewa da gaske yake game da sauyin na demoƙuraɗiyya inda ya sauka bayan cikar wa´adin mulkinsa.

"A ƙarshen wa´adin mulki na fata na shi ne duk wanda zai gaje ni ya hau mulki ta hanyar zaɓe na gaskiya da adalci ba tare da wata taƙaddama ba."

Wannan fata na sa ya tabbata domin zaɓan John Kufuor a muƙamin sabon shugaban ƙasa Ghana ta shaida wani sauyin mulki na demoƙuraɗiyya. Tun shekara ta 2001 Kufour ya gudanar da kyakkyawan shugabanci inda aka samu ƙaruwar ´yancin ´yan jarida da faɗin albarkacin baki da sannan yanzu akwai jam´iyun siyasa kimanin 20 yayin da yawan ´yan ƙasar dake fama da talauci ya ragu idan aka kwatanta da a 1990.

Duk da haka Ghana na fama da manyan matsaloli na magance yaɗuwar cutar AIDS da farfaɗo da tattalin arzikinta da ya dogara ga ɗanyun kayan da take sayarwa a ƙetare da kuma taimakon raya ƙasa da take samu. To sai dai gano rijiyoyin mai a ƙasar zai buɗe mata sabuwar hanyar samun kuɗaɗe shiga. Shugaba Kufour ya bayyana ra´ayinsa game da taimakon raya ƙasa kamar haka.

Ya ce: "Bai kamata taimakon raya ƙasa ya tsaya ga magance matsalolin talauci a ƙasashe masu tasowa ba, kamata ya yi ya ciyar da tattalin arzikinsu gaba."

Kufour dai ya tafiyar da kyakkyawar hulɗar dangantaka da sauran ƙasashen duniya saboda haka kamata yayi duk wanda zai gajeshi ya ci-gaba da inganta wannan kyakyawan haɗin kai tsakanin Ghana da sauran ƙasashen duniya.

Sauti da bidiyo akan labarin