1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wainar siyasar Yankin Gabas ta Tsakiya

Ibrahim SaniDecember 25, 2007
https://p.dw.com/p/CgAU

An tashi daga tattaunawar sulhu, a tsakanin Israela da yankin Falasɗinawa, ba tare da cimma tudun dafawa ba. Saɓanin hakan ya biyo bayan aniyar Israela ne na ci gaba da gina matsugunai, a yammacin kogin Jordan. Wakilan Falasɗinawa a tattaunawar, sun yi watsi da wannan mataki da cewa abune da ka iya mayar da hannun agogo baya. Tattaunawar ta Birnin Jerusselem ta kasance ta biyu ,aci gaba da tattaunawar sulhu, a tsakanin ɓangarorin biyu, bayan taron Annapolis da Amirka ta ɗauki nauyin shiryawa. A mako mai kamawa ne Faraminista Ehud Olmert da takwaransa na Falasɗinawa Mahmud Abbas, za su sadu don ci gaba da wannan tattaunawa. Shugabannin biyu za su tattauna matsalar dake kawo tsaiko ne aci gaba da tattaunawar sulhun, a tsakanin Israelan da kuma yankin na Falasɗinawa.