Wai Shin Da Gaske Ne Amurka Na Da Niyyar Kai Wa Iran Hari? | Siyasa | DW | 17.01.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Wai Shin Da Gaske Ne Amurka Na Da Niyyar Kai Wa Iran Hari?

A cikin wani rahoton da ta bayar mujallar "New Yorker" ta ce mahukuntan sojan Amurka sun tura wata tawaga ta 'yan kundumbala domin binciko wuraren da za a iya kai musu farmaki a kasar Iran

A hakika dai ba don cikakkiyar yardar da aka yi da Seymour Hersh a matsayinsa na dan jarida dake bin diddigin al’amura daga tushensu ba, to da kuwa ba wanda zai amince da wannan rahoto da ya bayar. Amma fa dan jaridar na mujallar "New Yorker" ya sha fallasa tabargaza iri dabam-dabam, inda da farko akan musunta bayanai da ya bayar, amma daga bisani sai gaskiya ta fito fili. Rahotonsa na baya-bayan nan dai yayi nuni ne da cewar yau kimanin watanni shida ke nan da mahukuntan sojan kundumbala na kasar amurka suka tura wata tawagar leken asiri, domin ta binciko wuraren da za a iya kai musu hare-hare a kasar Iran. Kuma kamar yadda aka saba, mahukuntan sojan na Amurka ba su yi wata-wata ba wajen karyata wannan rahoto, suna masu ikirarin cewar wai rahoton bai kunshi wasu cikakkun bayanai ba. Amma ayar tambaya a nan shi ne abin da ake nufi da cikakkun bayanai. Ko shin maganar cewa ‚yan kundumbalan na Amurka sun kutsa Iran ne ta kasar Pakistan ko kuwa cewar da yayi tuni shugaba Bush ya rattaba hannu akan takardar kutsen sojan Amurka a wasu kasashe goma da kuma cewar a idon Amurka kasar Iran wani babban fage ne na yaki. Bisa ga dukkan alamu dai shugaban kasar Amurka George W. Bush, wanda ake shirye-shiryen rantsar da shi a ranar alhamis mai zuwa, ba abin da ya sa gaba illa ya sake billo da wani sabon rikicin ko kuma ya kara tsawwala wanda ake fama da shi, a daidai wannan lokacin da ake ciki, inda wakilan hukumar makamashin nukiliya ta IAEA ke binciken tashoshin nukiliya na kasar Iran, sannan su kuma kasashen KTT a nasu bangare suke kokarin ganin an samu kusantar juna tare da fadar mulki ta Tehran. Shi dai shugaban na Amurka imani yayi cewar al’umar kasar sun sake zabensa ne domin su nuna goyan bayansu ga matakinsa na mamayar Iraki ba tare da wani dalili ba. Amma ita Iran ba kanwar lasa ba ce. Domin kuwa a yayinda dukkan ikirarin da aka yi na cewar Iraki na mallakar muggan makaman kare dangi ya zama tsabar farfaganda ko kuma wani gigin barcin da Amurka ta dade tana fama da shi, ita Iran akwai tabbatacciyar shaidar dake nuna cewar kasar ta samu kakkarfan ci gaba a kokarinta na harhada makaman kare dangi da sauran makamai masu linzami dake cin gajere da kuma dogon zango. Bugu da kari kuma duk da wannan ci gaba da kasar ta samu, babu wani dalilin da zai sanya a kai mata hari, saboda ta fito fili ta bayyana manufarta a game da tashoshinta na makamashin nukiliya, wadanda ta ce tana kokarin neman wata hanya ce ta dabam domin samun isasshiyar wutar lantarki. Take-taken na shugaba Bush na bayyanarwa ne a fili cewar ya rantse lalle sai ya ci gaba da ta da zaune tsaye a wannan shiyya, domin zama abin misali na kasancewar Amurka babbar daular duniya. A nan maganar demokradiyya ma ba ta taso ba, idan aka yi la’akari da abin dake wanzuwa a kasar Iraki, bayan mamayar da Amurka tayi wa kasar. Shi dai rahoton na Seymour Hersh ya kara jefa mutane cikin hali na dardar, su kuma Iraniyawa, murnarsu ta koma ciki dangane da fafutukarsu ta tabbatar da mulkin demokradiyya a kasarsu.