1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wai shin ƙungiyar leƙen asirin Jamus ta taimaka wa Amirka a lokacin yaƙin Iraqi kuwa ?

February 26, 2006

A halin da ake ciki yanzu dai, `yan adawa a majalisar dokokin tarayya na neman a gudanad da bincike kan zargin da ake yi wa ƙungiyar leƙen asirin Jamus, wato BND, na bai wa dakarun Amirka wasu muhimman labarai, waɗanda suka taimaka musu wajen kai hare-haren bamabamai a kan sojin Iraqi da kafofinsu.

https://p.dw.com/p/Bu1R
Majalisar dokokin Bundestag ta tarayyar Jamus.
Majalisar dokokin Bundestag ta tarayyar Jamus.Hoto: dpa

Game da ƙorafin da ake yi kan batun haɗin kan nan da ƙungiyar leƙen asirin Jamus wato BND ta bai wa dakarun Amirka a lokacin yaƙin Iraqi, gwamnatin tarayya ta ba da wata sanarwa inda ta ce, a halin da ake ciki a wannan lokacin, ƙungiyar ba ta da wanni zaɓi. Kuma ko da ta sami kanta cikin irin wannan halin ne a yanzu, za ta maimaita abin da ta yi ne. Wannan sanarwar dai na ƙunshe ne cikin wani rahoton da gwamnatin ta miƙa wa kwamitin bincike na Majalisar Dokokin Bundestag a kan wannan batun.

Sai dai shafi 90 daga cikin shafi ɗari 3 na rahoton ne aka bayyanar wa maneman labarai. Hakan kuwa, ya zama dole ne saboda jami’in kula da kiyaye batutuwan da suka shafi sirrin ƙasa na gwamnatin tarayya, ya hana a bayyana ababan da ke ƙunshe cikin sauran shafi ɗari 2 da goman, inji Olaf Scholz, shugaban reshen jam’iyyun jam’iyyun gwamnati a majalisar dokokin.

A taƙaice dai, abin da rahoton da aka bayyana wa maneman labaran ke ɗauke da shi, shi ne; ƙungiyar leƙen asirin Jamus ba ta zarce haddin aikinta a Iraqin ba, kuma duk wasu labaran da ta bai wa rundunar sojin Amirka a lokacin da ta kai hari a birnin Bagadaza, ba su da jiɓinta da yaƙin Iraqin da kansa. A halin da ake ciki dai jam’iyyun adawa a Majalisar na bukattar a gudanad da cikakken bincike ne a kan wannan batun don gano cewa ko lalle ne ƙungiyar leƙen asirin Jamus ta bai wa Amirka wasu muhimman labarai, wadanda suka taimaka mata wajen kai hare-hare a kan kafofin gwamnatin Iraqi a birnin Bagadaza. Amma ita gwamnatin tarayya na nanata cewa, ban da rahoton da ta miƙa wa kwamitin da aka kafa, duk wani yunƙurin samo ƙarin bayanai zai ci tura.

Duk da hakan dai, `yan jam’iyyun adawan sun dage kan cewa sai an gudanad da binciken. Wani ɗan majalisar, na jam’iyyar Greens Hans-Christian Ströbele, ya ce a cikin shekara ta 2003, ƙungiyar leƙen asirin ta Jamus, ta bai wa runudunar Amirka cikakken labarai kan wasu guraba 12, waɗnada kuma mai yiwuwa aka kai musu hare-haren bamabamai. Kamar dai yadda ya bayyanar a wata fira da ya yi da gidan talabijin nan na NTV:-

„`Yan ƙungiyar leƙen asirin sun ba da labarai kan wasu guraba, waɗanda ke da jiɓinta da harin da aka kai musu. Duk da cewa sun sanar da mahukuntan Jamus, amma an miƙa duk wasu muhimman labaran ga Amirka, wadanda ke ɗauke da cikakkun bayanai kan inda guraban suke. A lal misali, ramukan kuran sojin Iraƙin tare da makamansu na yaƙi.“

Gwamnatin tarayya dai ba ta yi musun cewa wasu labaran na ɗauke da batutuwan da suka shafi harkar soji ba. Sai dai ta ce, ba su isa ba, wajen bai wa dakarun Amirkan damar kai hare-haren bamabamai a kan guraban. To wannan daddagewar da gwamnatin tarayya ke yi wa yunƙurin kafa kwamitin bincke a majalisar dokoki dai, ya janyo rarrabuwar hankullan jam’iyyun adawan. Ba dukkansu ne suka ba da sanarwar amincewa da kafa kwamitin ba. Har ila yau jam’iyyar FDP ba ta yanke shawarar goyon bayan shirin ba tukuna. Ana dai kyautata zaton cewa, idan aka kafa kwamitin, to zai kuma gudanad da bincike kan batun jigilar fursunoni daga nan Jamus da ake tuhumar ƙungiyar leƙen asirin Amirka, wato CIA da aikatawa, tare da yin garkuwa da wani ɗan ƙasar Jamus mai asali daga ƙasar Lebanon, El-Masri da ta yi.