WAHALHALUN DA YARA KANN FADA CIKI | Siyasa | DW | 02.12.2003
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

WAHALHALUN DA YARA KANN FADA CIKI

A cikin matsalolin da yara kan fuskanta, dai, akwai, batun shirga masu ayyukan da suka fi karfinsu. Sannan kuma a wasu lokuttan akan samu wadansu jama'ar dake safarar kananan yara a matsayin wadanda za'a bautar da su. A Nigeriya, 'yan sanda sun bankado irin wannan shirin, a inda wadansu miyagu, suke aikin safarar yara tsakanin kasashe, kamar yadda Sam Olukoya, ya ruwaito mana, daga Lagos. A cikin samamen da 'yan sandan Nigeriyar suka kai, sun samu watsa wani shirin shiga cikin wannan kasar ta Nigeriyar,da yara kimanin 200, daga kasar Benin, dake makwabtaka da Nigeriyar. Yaran da aka samu cetowa daga miyagun mutanen, yara ne, 'yan shekaru daga 5 zuwa 15,a bisa yadda wadannan mutanen ke sato yara daga iyayensu, ko kuma, su yaudari iyayen yaran da cewar, wai zasu kaisu Nigeriya,ne, su samu karatu mai inganci, a cikin makarantun Nigeriyar, alhali kuwa, zasu kaisu ne, wajen ayyukan bauta kurum. Yaran dai, da aka samu kubutarwar, daga hannun wadannan miyagun mutanen, sun bayyana cewar, an kaisu cikin wani kungurumin daji ne. Daya daga cikin yaran, Macenia Boha, ya ce ko abincin kirki ba'a basu, a cikin dajin da suke. Yaron yace, da zarar sun nemi, a basu abinci, sai a rika fada masu cewar, aikin mi sukayi, da za'a basu abinci. Yace mafi yawan lokaci, suka kasance ne a cikin yunwa, sannan ga azabar aikin da ake sanya su yi, na wahala,irin na fasa duwatsu na gini, da tara yashin gini, sannan ga dukansu da akeyi,a cikin irin azabobin da suke sha.Sannan sukan kamu da rashin lafiya iri iri. Alexis Kesinu, dan shekaru 10 da haihuwa, yace akwai yaran da sukayi ta rasa rayukan su, a cikin wannan halin da aka sanyasu. Da zarar yaran sun koka akan yanayin da suke samun kansu ciki, ga wadannan miyagun mutanen da ke azabtar dasu din, sai mutanen su rinka cewa, wai yaran suna karya ne.

Aikin tara yashin da yaran keyi, dai, da kuma, fasa duwatsun, sune, ake kwasa tipa tipa, ana kaiwa gari gari ana sayarwa masu ayyukan gine gine, a Nigeriya, kamar yadda binciken, da Sam Olukoyan yayi, ya nunar. Yaran dake cikin wannan waahalar dai, sun dade suna cikin wannan halin, a cikin dazuzzukan dake sashen kudu na Nigeriyar, da aka tarasu a wurin, har sai kimanin shekaru 7 baya ne, aka fara lura da wannan mugunyar dabi'ar dake gudanan, a wannan yankin. An kuwa samu damar sanin halin da ake cikin ne, bayan wadansu mutane, na kirki, sunyi ta rubutawa da aika kara akan yadda ake cin mutuncin yaran, ana bautar dasu. Wannan ne, ma ya sanya, a halin yanzu,'yan sanda a Nigeriyar suka samu nasarar,kubutar da yara fiye da 200, yayin da aka kame mutane 7, a bisa zargin sune jigajigan, tafka wannan mugun aikin. A halin yanzu, dai, akwai wadanda suka tsere tare da dubban yara,a yankin kudu maso yamman a Nigeriyar,da ake cikin neman su, har yanzu, ba'a samu kamesu ba.

Sufeto janar na 'yan sandan Nigeriya dai, ya lashi takobin watsa wannan kungiyar miyagun, domin kawar da wannan muguwar dabi'ar ta bautar da yara, a Nigeriya.
 • Kwanan wata 02.12.2003
 • Mawallafi ABUBAKAR D. MANI
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvnH
 • Kwanan wata 02.12.2003
 • Mawallafi ABUBAKAR D. MANI
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvnH