1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wadanne Kasashe ne suka haramta shan taba

Abba BashirMarch 28, 2007

Kasashen da suka haramta shan taba a bainar jama’a

https://p.dw.com/p/BvUt
Wani yana shan Taba
Wani yana shan TabaHoto: AP

Jama'a masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na wasikun ma su sauraro,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun mai sauraron mu a yau da kullum, Malama Kyauta Yunusa, Birnin Yamai , dake Jamhuriyar Nijer; Malamar tana tambayane akan cewa; Wadanne kasashe ne suka haramta shan taba sigari a bainar jama’a?

Amsa: Shan taba sigari yana kara zama wata dabi’a ta kadaici, kasancewar yanzu mutane suna kara fahimtar illar da hayakin taba yake haifarwa, sakamakon zama tare da mai shan taba a lokacin da yake/ take shan tabar.Kasashe da dama dai a yanzu haka sun kafa dokar hana shan taba sigari a bainar jama’a, domin kare yanci da lafiyar mutanen da basa shan tabar.

Daga cikin kasashen da suka haramta shan tabar a bainar jama’a dai, akwai Kasar Australia, Belgium, Bermuda, Bhutan, British Virgin Islands, Canada, Cuba da Denmark. Duk wadannan kasashe dokar tasu zata fara aikine daga watan Aprilu na wannan shekara ta 2007.Sai kuma rukunin kasashen France, Hong Kong da Iceland. Wadanda dokar tasu zata fara aiki a watan Yuni na wannan sheka.

Sai kuma ajin Kasashen India, Iran, Ireland, Italy, Latvia, Lithuania, Malta, Malaysia, Montenegro, New Zealand, Norway da Puerto Rico. Su kuma dokar tasu ta fara aiki ne a wannan wata na Maris da muke ciki. Akwai kuma rukunin kasashen Singapore, South Africa, Sweden, Uganda, United Kingdom da Uruguay.Inda su kuma dokar tasu zata fara aiki daga watan Yuli na wannan shekara ta 2007.

To akwai kuma kasashen da basu haramta shan tabar a bainar jama’a ba, amma dai sun kebe wasu wurare inda aka haramta shan tabar, wuraren kuwa sune;Ofisoshin gwamnati da Asibitoci da kuma tashoshin mota.Wadannan kasashe dai sune; Armenia, Bangladesh, Chile, Czech Republic, South Korea, Spain, Tanzania, Thailand, Turkey, da Vietnam.

A kasar Amurka kuwa, an samu wata kasida wadda take bayani game da yancin Amerikawa marasa shan taba sigari,inda take nuna cewa wasu daga cikin jihohin Amurka sun haramta shan taba sigari a wuraren aiki da kuma gidajen cin abinci. Wadannan jihohi sun hada da ; Arizona, Wadda dokar tata zata fara aiki a watan Mayu na 2007, sai kuma Jihohin California, Colorado, Connecticut, Delaware, District of Columbia, Florida, Hawaii, Idaho, Louisiana, Maine, Massachusetts, Montana, Nevada, New Jersey, New York, North Dakota, Ohio, Rhode Island, South Dakota, Utah, Vermont, da Washington.