Wadanda suka rasu sakamakon ambaliya a Habasha ya kai mutum 900 | Labarai | DW | 18.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wadanda suka rasu sakamakon ambaliya a Habasha ya kai mutum 900

Hukumomi a Habasha wato Ethiopia na kokarin kaiwa ga dubban mutane da ambaliyar ruwa ta yiwa kawanya a sassa daban daban na kasar. Alkalumman da aka bayar baya bayan nan sun nunar da cewa akalla mutane 900 suka rigamu gidan gaskiya sannan wasu daruruwa sun bata sakamakon wannan ambaliyar ruwa. Yankin da wannan bala´i ya fi shafa na cikin wani yankin karkara na kudancin kasar, inda kogin Omo ya cika har ya batse, sannan ruwa ya malala cikin akalla kauyuka 14. Gwamnati a birnin Addis Ababa ta yi kira ga kasashen duniya da su kai mata dauki cikin gaggawa.