1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wacece Shugabar Kasa ta farko

Abba BashirSeptember 11, 2006

Bayani akan Shugabannin kasa Mata a Duniya

https://p.dw.com/p/BvVG
Angela Merkel ta Jamus
Angela Merkel ta JamusHoto: AP

Jama’a masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya:Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun,malama Bilkisu Nasiru, Garin Bauchi a Jihar Bauchi dake tarayyar Najeriya. Malamar cewa ta yi; Wace mace ce Shugabar Kasa ta farko a Duniya, kuma a yanzu haka Kasashen Duniya nawa ne, wadanda Mata suke a Matsayin Shugabanni?

Amsa: To Shugabar kasa ta farko, ko kuma ace Firaminista ta farko a Kasashen Duniya, ita ce Madam Suhbaataryn Yanjmaa, wadda aka haifa a shekarar 1893 ta kuma rasu a shekarar 1962, lokacin tana Yar shekara 69 da haihuwa. An zabi Madam Suhbaataryn a matsayin shugabar Kasar Mangoliya a shekarar 1953. To tun daga wannan lokaci ne fa, Mata suke ta shiga fagen siyasa ana damawa da su, ta haka yasa aka yi ta samun karuwar Mata shugabanni a kasashe daban-daban a wannan Duniya.Fitattu daga cikin su sun hada da Margaret Thatcher ta Birtaniya da Edith Cresson ta Faransa da kuma Corazon Equino ta Philippines.

Idan aka koma batun Mata wadanda suke Mulkin Kasashensu a halin yanzu, to sai muce, a yau dai ba a gobe ba, akwai Kasashe 12 a Duniya da Mata ne suke shugabancinsu, ko dai a matsayin Shugabar Kasa, ko shugabar Gwamnati, ko kuma Firaminista.

Ga dai wadannan Kasashe, da kuma Matan da suke Mulkin su kamar haka;

Michelle Bachelet ta Chile

Helen Clark ta New Zealand

Luisa Diogo ta Mozambique

Tarja Halonen ta Finland

Myeong Sook Han ta South Korea

Ellen Johnson-Sirleaf ta Liberia

Gloria Macapagal-Arroyo ta Philippines

Mary McAleese ta Ireland

Angela Merkel ta Germany

Portia Simpson-Miller ta Jamaica

Dr. Vaira Vike-Freiberga ta Latvia

Khaleda Zia ta Bangladesh