Wace ala′ƙa ce tsakanin ido da kyamara | Amsoshin takardunku | DW | 12.02.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Wace ala'ƙa ce tsakanin ido da kyamara

Bayani game da baiwar da ke tattare da ido da kuma alaƙarsa da kyamara

default

Hoton idanun mutum

Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fito ne daga hannun malam Mudassir Ashafa daga Jihar Kaduna a tarayyar Najeriya. Malamin cewa ya yi; Don Allah Deutsche Welle ina so ku gaya min abubuwan aljabin dake tattare da halittar ido, kuma shin dagaske wai Bature ido ya kwaikwaya ya ƙirƙiri kyamara? Har ila yau ina so ku gaya min dangantakar dake tsakanin ido da kyamara.

Amsa: Babu shakka ba wai kyamara kadai ba, kusan dukkanin abubuwan fasaha da kimiyya da Bature ya ƙera, to ya kwaikwayi wata halittace ta ubangiji. A kwai abubuwan ban al'ajabi da dama dangane da halittar ido. Yanzu haka a 'yan mintina da suka wuce da fara wannan shiri namu, aƙalla fiye da ayyuka biliyan dubu sun faru a cikin idanuwanmu, kuma inda mutum ya san abubuwan da suke faruwa waɗanda suke baiwa idonsa ikon ƙiftawa, da kuma abubuwan da suke faruwa yayin da yake jujjuya idanunsa wajen kallon abubuwa daban-daban, cikin ɗan lokaci ƙalilan, to da wani zai iya cewa ma a duk halittar da Allah yai a jikin mutum babu abin da ya fi ido ban mamaki. Idan akai nazari tun daga gashin ido zuwa fatar ido zuwa ƙwayar ido da abuwan dake cikin idon waɗanda suka haɗu suka haifar da gani, abubuwa ne na ban al'ajabi suke faruwa ba tare da mutum ya sani ba.

Muɗauki misalin gashin ido, shin ko mutum ya taɓa tunanin ni'imar dake tattare da gashin ido? ƙaddara ace an bar gashin ido yana toho kamar gashin kai, ace babu wani tsari da mahaliccin ido ya halitta wanda zai hana gashin ido ci-gaba da toho, to yaya mutum yake zaton zai tsinci kansa? Kafin ma ayi batun kariya da gashin idon yake baiwa idanu daga faɗawar abubuwa cikin ido irin su gashi ko ƙura ko kuma ɓurɓushin wani abu.

Haka idan muka je ga fatar ido, mutane sukan ƙifta idonsu sau dubban lokaci a rana ba tare da sani ba. To wannan fata ta saman ido ita ce mataki na biyu na kariya ga ido wajen hana shigar wani datti ko burbuɗin wani abu. Sannan kuma akwai wasu sinadarai na musamman da akodayaushe suke tabbatar da cewa cikin fatar bai rabu da danshi ba, don haka a duk lokacin da mutum ya kifta idonsa to kamar yana goge idon ne. Kamar dai yadda magogin gilashin dake gaban direban mota yake aikin wanke gilashi idan ana ruwa ko kuma domin goge datti. Da ace fatar ido ba tai dai-dai da ƙwayar ido ba, to da wataƙila ba za ta iya goge idon gabaɗaya ba, kuma da ba zai taɓa yiwuwa mutum ya goge dattin da ya tattaru a cikin idonuwansa gaba ɗaya ba. To kuma a ƙaddara ma fatar ba da kanta take wannan aiki ba, sai datti ya taru sannan mutum zai farga ya goge ko kuma ace babu fatar idon duk abin da ya taho haka zai faɗa kaitsaye, babu shakka da rayuwa ta yi wahala ƙwarai, amma mutane da dama ba su damu da tunanin wannan ni'ima ba.

Haka zalika hawaye na da matuƙar muhimmanci ba wai lallai sai na kuka ba, shi ya sa idan wani abu yai wuf ya faɗa ido kaitsaye, nan da nan sai hawaye su zubo dai-dai gwargwado yadda za su taimaka wajen kore wannan datti da ya faɗa cikin ido. Kuma hawaye suna kare ido daga kamuwa da cututtuka, hasalima wannan ɗanɗanon gishiri-gishirin da ake ji a cikin hawaye to wani sinadari ne mai kashe ƙwayoyin cuta na cikin ido wanda ƙarfinsa ya fi na sinadarin kashe kwayoyin cuta irin wanda ake amfani da shi a banɗaki, amma sai mahaliccin ido ya daidaita shi yadda zai yi daidai da ido batare da ya cutar da shi ba.

To idan muka yi nazarin yadda aka tsara gani ya tabbata, za mu ga cewa, tun ɗan Adam yana cikin mahaifa, mahaliccinsa ya tsara masa yadda tsarin ganinsa zai kasance. Kuma an tsara gani akan yadda ƙwaƙwalwa zata iya ajiye abin da mutum ya gan shi ya kuma san shi. Misali abubuwan da mukan iya tunawa a rayuwarmu kamar su yarintarmu, makarantun da muka taɓa yi, gidajen da muka sani, muna gane su ne ta hanyar ganinsu da muka taɓa yi da kuma zama da suka yi a wani ɗan ƙanƙanin bigire a ƙwaƙwalwarmu. Gane rahamar wannan ni'ima zai yiwu ne kawai idan mutum yai tunanin cewa, yanzu ace duk abin da mutum ya taɓa gani komai sanin da kai masa, sai ace kuma idan ka ɗauki wani lokaci shike nan ka manta shi, kuma ko da ka sake ganinsa ba za ka iya tuna cewa ka sanshi ba, to ai da rayuwa ta shiga ruɗu ƙwarai. Kuma sau tari irin wannan na faruwa a cikin al'umma, amma a wasu lokuta musamman ma a rayuwa irin ta Afirka, sai ace mutum ya samu taɓin hankali. Ma'ana yakan kasance sakamakon wani hatsari da mutum ya yi, sai ya ɗan samu rauni a ƙwaƙwalwarsa, to idan wannan rauni ya faru ne a bigiren da ake ajiye abubuwan da mutum ya taɓa gani a rayuwarsa, to babu shakka duk bayanan abubuwan da mutum ya taɓa gani za su goge, akan haka sai aga mutum ya manta kowa nasa, ko da kuwa iyayen mutum da matansa da 'ya'yansa da masoyansa, mutum baya iya gane su. To anan Turai akan yi maganin irin wannan larura ta hanayar ɗaukar lokaci mai tsawo, wani sa'in ma shekaru ana renon mutum ta hanayar nuna masa wasu abubuwa na rayuwa har mutum ya warke sosai. Amma a Afirka sai a bar mutum yai ta watangaririya ace wai ya taɓu. Wata ƙila ma saboda wannan muhimmanci da ƙwaƙwalwa take da shi, shi ya sa anan Turai ba'a taɓa hawa keke ko babur sai da hular kwano, saboda koda hatsari ya faru to ƙwaƙwalwa dai ta tsira. Domin idan ta taɓu to dukkan jiki ya taɓu.

Mutum ya tsinci kansa ne an haife shi da idanu biyu, amma mutane da yawa ba su taɓa tunanin dalilin haka ba. Domin a haƙiƙa kowane ido cin gashin kansa ya ke yi, kuma zai iya gani ba tare da taimakon ɗaya idon ba. Don haka wani ma zai iya cewa , to idan haka ne mene ne amfanin idanuwa biyu.

To amfanin kasancewar idanuwa biyu shi ne. Idanun mutum an haliccesu ne kuma aka sanya aƙalla tazarar santimita 5 tsakanin ido da ido. Amma kowanne ido yana da wata baiwa da ɗayan bai da ita wajen ganin abubuwan duniya. Akwai abubuwa uku da suke haɗuwa su bayar da cikakken gani; na farko shi ne iya nisan da ake iya gani ta gefen dama, na biyu shi ne iya nisan da ake iya gani ta gefen hagu, na uku kuma shi ne nisa ko zurfi da mutum ke iya gani kai tsaye ta gabansa. To ƙwayar ido guda ɗaya tana iya kallon surar abu ne kawai ta ɓangarori biyu wato dama da hagu. To akwai wani abin mamaki dake faruwa anan. Ita ƙwaƙwalwa ita ce take haifar da ɓangare na uku na gani wato zurfi. Kuma tana yin haka ne ta hanyar haɗa surar abin da idanuwan biyu suka ɗauko tare domin a samu cikakken gani. To ta hanyar tantance banbancin abin da kowanne ido ya ɗauko ne ƙwaƙwalwa take tantance zurfi ko nisan abu, yadda surar abin za ta fita dai-dai mutum ya gani radau. In ba don wannan aiki da ƙwaƙwalwa take yi ba, to da sai mutum ya riƙa ganin surorin abubuwa bi-biyu bi-biyu. Ba tare da tantance zurfi ba.

Za mu iya tabbatar da wannan batu ta hanayar buga misali. Yanzu ace mutum yana kallon rassan wata bishiya da ke gabansa, farko sai ka kalle ta da duk idanunka biyu a buɗe. Bayan ɗan lokaci kaɗan sai ka rufe ido ɗaya sai ka riƙa bin rassan bishiyar da kallo da ido ɗaya, to bayan kamar minti ɗaya kuma sai ka buɗe ɗaya idon, za ka fahimci cewa rassan bishiyar sun ɗan yi zurfi ba kamar yadda kake kallonsu da farko ba. Misali na biyu kuma shi ne, ka jarraba sanya zare a cikin allura da idonka ɗaya a rufe, za ka ga cewar ba za ka iya ba, saboda da gani na ido ɗaya kaɗai ba za ka iya halarto zurfin da ke tsakanin allura da zaren ba. Saboda haka surori biyu da kuma ƙirƙirar ɓangare na uku na gani su suke haifar da cikakken ganin abu a cikin cikakkiyar sura. Godiya ta tabbata ga wanda ya halicci gani.

To idan muka koma ga batun alaƙar da ke tsakanin ido da kyamara a taƙaice, za mu iya cewa, alaƙa ce ta cewa daga ɗaya aka kwaikwayi ɗaya. Wato daga ido aka kwaikwayi kyamara. Amma dai duk da haka idan aka kwatanta su za a gane cewa banbancin a bayyane yake. Kaɗan daga cikin miliyoyin misalan da za a iya bayarwa shi ne cewar, Na farko dai, mu ce saiti. Kyamara sai an saita, ido kuwa shi yake saita kansa da kansa. Haka zalika idan muka ɗauki nisa, ido shi ke daidaita nisan abu da kansa amma kyamara sai an daidaita ta. Kyamara a masana'anta aka ƙera ta, shi kuwa ido a cikin mahaifa aka halicce shi. A tafiye kyamara ba za a ɗauki hoto ta fitar da shi kar-kar ba, za a ga hoton ya yi rawa, amma ido ko a tafiye kar-kar yake gani in dai mai cikakkiyar lafiya ne. Ido na da sinadaran hawaye da suke masa wanki na musamman, kyamara kwa sai dai a sa sinadarin a goge. Dadai abubuwan da ba za su lissafu ba idan ana batun danganta kyamara da Ido.

Dukkan abubuwan da muka tattauna game da ido suna nuna irin abubuwan al'ajabi da suke faruwa a ido waɗanda suke baiwa mutum ikon gani: Kama dai daga kasancewar kwayar ido zuwa yadda idon yake karɓar haske, zuwa samuwar hawaye da kuma jijiyoyin da suke kai sako daga ido zuwa ƙwaƙwalwa, da yadda aka tsara halittar gani da bigiren da ganin yake tabbata, har ake iya ganin abin da ya kamata a gani ɗin. Wannan ya tabbatar mana da cewa halittar ido aiki ne na wani ƙasaitaccen masani mara misaltuwa, wato Allah mahaliccin kowa da komai. Wanda idan ya yi nufin yin halitta, sai ya ce da ita kasance, kuma ta kasance.