Waádin janye sojin Amurka daga ƙasar Iraqi | Labarai | DW | 26.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Waádin janye sojin Amurka daga ƙasar Iraqi

Majalisar wakilan Amurka ta amince da tsabar kuɗi dala biliyan 100 wajen tafiyar da ayyukan sojin Amurka a ƙasashen Iraqi da Afghanistan, to amma ta buƙaci janye ɗaukacin sojojin Amurkan daga Iraqi nan da ranar 31 ga watan Maris na shekara mai zuwa. Yan jamíyar Dimokrats masu rinjaye a majalisar sun kaɗa ƙuriár duk da adawa da wannan mataki daga shugaba George Bush. Tun da farko kwamandan sojin Amurka a Iraqin janar David Petraeus ya baiyanawa yan majalisar cewa a yanzu an sami raguwar kashe kashe a birnin Bagadaza musamman waɗanda ke da nasaba da ɗarika.