1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Waɗanne ne sababbin abubuwa bakwai mafiya ban mamaki a Duniya

December 4, 2007

Bayani game da sababbin abubuwa bakwai mafiya ban mamaki a Duniya

https://p.dw.com/p/CWNT
Machu Picchu, PeruHoto: picture-alliance/dpa

Masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkanmu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Amsoshin takardunku, shirin da a kowane mako yake amsa wasu daga cikin tambayoyin da kuka aiko mana.

Abdullahi: Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun Malam Nura Abdu Ɗan-bekuta Ƙofar sauri daga Jihar Katsina a Najeriya. Malamin tambaya ya yi , wai shin waɗanne abubuwa ne na ban al’ajabi guda 7 a Duniya, kuma a ina suke.

Abba: To ko da dai malam Nura bai fayyace tambayar tasa sosai ba, domin akwai abubuwan ban al’ajabi a Duniya guda 7 na tarihi, akwai kuma sababin abuwa 7 waɗanda suka fi ban mamaki a Duniya , wanda hakan wani ƙoƙari ne na ƙirƙiro wasu abubuwan ban mamaki domin su maye gurbin tsofaffin, kasancewar shida daga cikin bakwan na tsofaffin sun ɓace, abin da yai saura kawai ita ce Dalar Giza da take Ƙasar Misra.

Sakamakon haka ne ya sa aka shirya wata hanya ta kaɗa ƙuri’a ga duk Duniya, ta amfani da na’ura mai ƙwaƙwalwa, a ƙarkashin wata ƙungiya mai zaman kanta ta musamman da ake kira (New Open World Corporation) a Turance. To bayan an kaɗa ƙuri’ar ne aka sanar da abubuwan da suka sami nasara a ranar 7 ga watan Yuli, 2007 a birnin Lisbon dake ƙasar Portugal.

Abubuwan da aka sanar a ƙarshen zaɓe a matsayin mafi ƙololuwar abubuwan ban mamaki da ɗan Adam ya gina da hannunsa sune;

1.Ginin Taj Mahal na Ƙasar Indiya

2.Ƙasaitacciyar katangar ƙasar Chaina, wandda aka fi sani da suna “Great Wall of China’’ a Tutance.

3.Mutum mutumin Yesu al-Masihu dake Ƙasar Brazil, Wanda aka fi sani da suna “Christ the Redeemer’’ a Turance.

4.Wani Birnin kan tsauni da ake kira (Machu-picchu) a Ƙasar Peru.

5.Sai kuma Birnin da ake kira da suna (Chichen Itza ) wanda aka gina a siffar dala a Ƙasar Mexico.

6.Gidan Tarihi na Petra da ke birnin Jordan.

7.Sai hamshaƙin Dakin Taro dake birnin Rum a Ƙasar Italiya, Wanda aka fi sani da “Colosseum’’ a Turance.

Waɗanna dai sune abubuwa bakwai da aka yarda da cewa ɗan Adam ya nuna gwaninta wajen gina su a wannan Duniya tamu.

Wannan ƙungiya dai ta ƙasar Swiss da ta gudanar da wannan zaɓe, ta sanarwa da Duniya cewa, an kaɗa ƙuri’u fiye da miliyan 100 ta hanyar Yanar Gizo wato Internet, da kuma ta wayar Tarho. Ko dadai an kira wannan zaɓe da cewa ba sahihi bane saboda ba’a samar da wata kariya da zata hana wani mutum ya kaɗa ƙuri’a fiye da sau ɗaya ba. To amma dai sun tabbatar da cewa waɗanda aka zaɓa ɗin sune aka sanarwa da Duniya.