1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Vettel ya yi musu fintinƙau

Sebastian Vettel ya kafa tarihi a gasar tseren motoci na rukunin Formula-1

default

Sebastian Vettel, zakaran duniya a tseren Formula-1

Bajamushen nan ɗan tseren motoci a rukunin Formula-1, Sebastian Vettel mai shekaru 23 a duniya shi ya lashe gasar duniya ta tseren motoci na wannan rukuni a wannan shekara. A cikin motarsa ta haɗin guiwa tsakanin kamfanin Red Bull da Renault, tun da farkon fara gasar ta ƙarshe a Abu Dhabi ya yiwa abokan karawarsa fintinƙau. A jimilce ya samu yawan maki huɗu fiye da na mutumi mafi kusa da shi wato Fernando Alonso matuƙin motar Ferrari, wanda gabanin tseren ƙarshen na jiya yake kan gaba. Wannan nasarar da wannan matashi ya samu ya sa ya zama matashi mafi ƙarancin shekaru da ya taɓa lashe wannan gasa ta motoci masu ɗan karen gudu, wato kenan ya kafa tarihi a wannan rukuni. Shi ne kuma Bajamushe na biyu baya ga Michael Schumacher da tauraronsa ke haskakawa a tseren motocin na Formula-1. Shugabanni a nan Jamus sun yi aike masa da saƙon taya murna. A saƙonta gareshi, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce Vettel mai shekaru 23 tuni har ya kafa tarihi a fagen wasanni a duniya.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Abdullahi Tanko Bala