Venezuwela: Paparoma na son lamura su inganta | Labarai | DW | 11.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Venezuwela: Paparoma na son lamura su inganta

Shugaban darikar Katolika na Duniya Paparoma Francis ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta sa baki wajen ganin an warware rikicin siyasa da na tattalin arziki na kasar Venezuwela.

Fafaroma ya ce irin halin da mutane ke ciki na da ban tausayi domin kuwa irin matsin da ake fuskanta ya sanya da dama kauracewa kasar yayin da wanda ba za su iya ficewa ke cigaba da dandana kudarsu. Shugaban na darikar Katolika na wadannan kalamai ne bayan kammala wata ziyara ta kwanaki biyar da ya kai yankin Latin Amirka inda a jiya Lahadi ya gudanar da wani taron addu'a na musamman domin samun warwarewar lamura a kasar.