1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Venezuwela: Maduro ya lashe zaben shugaban kasa

Gazali Abdou Tasawa
May 21, 2018

Hukumar zaben Venezuwela ta bayyana cewa Shugaba Nicolas Maduro ya lashe zaben shugaban kasa na ranar Lahadi da kusan kaso 68 cikin dari na kuri'un da aka kada a zaben.

https://p.dw.com/p/2y3l4
Venezuela Wahlen - Nicolas Maduro
Hoto: picture-alliance/AP Photo/A. Cubillos

A Venezuwela Shugaba Nicolas Maduro ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a jiya Lahadi a wani sabon wa'adi na tsawon shekaru bakwai da zai ba shi damar shugabancin kasar har zuwa shekara ta 2025. 

Sakamakon da hukumar zaben kasar ta bayyana ya nunar da cewa shugaban mai akidar gurguzu ya lashe zaben da kashi 67,7 daga cikin dari a yayin da abokin hamayyar tasa Henri Falcon ya samu kashi 21,2 daga cikin dari na kuri'un da aka kada. Sai dai kuma tuni dan takarar da ya sha kayi ya yi watsi da sakamakon zaben yana mai zargin an tafka magudi a cikinsa tare da sayen kuri'un jama'a: O-Ton Falcon....

Ya ce "ba za mu amince da wannan sakamakon zabe ba domin ba a kiyaye ka'idoji da dama ba dan haka a wurinmu wannan zabe tamkar a a yi shi ba, kuma ya kamata a sake zaben kwata-kwata."

Daga nashi bangare Shugaba Maduro dan shekaru 55 ya bayyana gamsuwarsa da lashe zaben yana mai alfahrin samun yawan kuri'un da wani dan takarar neman shugabancin kasar bai taba samu ba a tarihin zabukan kasar