1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Venezuwela: An zargin adawa da yinkurin juyin mulki

Gazali Abdou Tasawa
October 4, 2017

Gwamnatin Venezuwela ta zargi madugun 'yan adawar kasar Leopoldo Lopez da kasance da hanunsa a yinkurin kifar da Shugaba Nicolas Maduro.

https://p.dw.com/p/2lAcE
Venezuela Oppositionsführer Leopoldo Lopez
Hoto: Imago/PanoramiC

Gwamnatin Venezuwela ta zargi madugun 'yan adawar kasar Leopoldo Lopez da kasance da hanunsa a yinkurin kifar da Shugaba Nicolas Maduro. Ko baya ga Leopoldo Lopez wanda da ma ake tsare da shi a gidansa tun a watan Yulin da ya gabata, gwamnatin ta kuma zano Oscar Perez tsohon dan sandar nan da ake zargi da kai hari da gurneti a kotun kolin kasar a watan Yunin da ya gabata da kasancewa da hannu a cikin yinkurin juyin mulkin.

Mataimakin shugaban kasar ta Venezuwela Tareck El Aissami ya sanar da hakan a gidan radiyo da talabijin na kasar inda ya kara da cewa sun mallaki hujjoji na yadda aka kitsa yinkurin juyin mulkin da kuma mutanen da ke da hannu a ciki da suka hada da Manuel Chacin mamba a jam'iyyar Voluntad Popular wacce Leopoldo Lopez din ya kafa. 

Sai dai kuma jam'iyyar ta Voluntad Popular ta fitar da wata sanarwa inda ta nisanta kanta da mutuman wanda ta ce ba shi da wata alaka da jam'iyyar.