Venezuela ta gargadi Amirka kan harkokin siyasa
December 1, 2007Shugaba Hugo Chavez na Venezuela ya gargadi Amirka da daina katsalandan, a harkokin siyasa a ƙasar. Gargadin ya zo ne kwana ɗaya a gudanar da zaɓen raba gardama, a game da ƙoƙarin yiwa kundin tsarin mulkin ƙasar kwaskwarima. Goyon bayan da Amirka ke ba wa ´Yan adawa na ƙasar a cewar Mr Chavez, abune da ka iya gurgunta zaɓen da ake shirin gudanarwa a gobe lahadi. Mr Chavez ya kara da cewa Venezuela a shirya take ta mayar da martani ga Amirka ta hanyar katse man da take bawa ƙasar. Batun kawo ƙarshen wa´adin shugaban ƙasa da kuma cikakken ikon shugaban babban bankin ƙasar na daga cikin abubuwan da za a yiwa kwaskwarima, a cikin kundin tsarin mulkin ƙasar. Hakan dai a cewar masu nazarin siyasa, ka iya bawa shugaban damar yin ta zarce a karo na uku a jere.