1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Venezuela ta dangana da samun kujerar komitin Sulhu

October 25, 2006
https://p.dw.com/p/Buef

Bayan taci-bata ba taci ba,da aka sha yi ,a zaɓen raba gardama, tsakanin ƙasashen Venezuella, da Bolivia, a takara kujera komitin sulhun Majalisar Ɗinkin Dunia, a ƙarshe Venezuela, ta dangana, da samun wannan matsayi.

Sanarwar ta hito daga fadar shugaban ƙasar Bolivia, Evo Morales.

Idan dai ba a manta ba , an yi zaɓe har zagaye 35, a makon da ya gabata, domin hida gwani tsakanin ƙasashen 2, domin wakiltar yankin Latine Amurika, a komitin sulhu na Malalisar Ɗinkin Dunia, ba tare da an cimma nasara ba.

Sakamakon ƙuri´un, a ko da yaushe, na jera ƙasashen 2 a kunnen doki.

Nan gaba a yau, Majalisar Ɗinkin Dunia ke kaɗa sabuwar ƙuri´a, karo na 36.

To saidai ya zuwa yanzu, ƙasar Venezuela, da Amurika ta azawa karan tsana, ba ta hito hili ba, ta gaskanta sanarwar janyewar ta daga samun wannan kujera.