Venezuela ta ce farashin gangan man fetur zai iya kai dola 100 nan gaba. | Labarai | DW | 28.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Venezuela ta ce farashin gangan man fetur zai iya kai dola 100 nan gaba.

Ministan harkokin man fetur na ƙasar Venezuela, Rafael Ramirez, ya ce nan gaba farashin gangan man zai iya kai dola ɗari. Da yake fira da gidan talabijin nan Telesur jiya daddare, ya ce duk da hauhawar farashin da ake samu a yanzu, matsalar ba ta kai ta rikicin shekarun 1970 ba.

Sai dai matsalar da ake huskanta yanzu ita ce gwagwarmaya tsakanin ƙasashen da ke samad da man fetur ɗin da kuma ƙasashe mafi amfani da shi. A nasa ganin dai, ba za a iya dawowa a matsayin da ake sayar da gangan man fetur ɗin a dola 20 ba.