1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Venezuela: Maduro na son ganawa da Shugaba Trump

Salissou Boukari
August 11, 2017

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya sanar cewa da a shirye yake da tattauna da shugaban Amirka donald Trump indan har da gaske yake yana da ra'ayin kasar ta Venezuela.

https://p.dw.com/p/2i2tR
Venezuela - Präsident Nicolas Maduro
Shugaban kasar Venezuela Nicolas MaduroHoto: Reuters/U. Marcelino

Shugaba Maduro na Venezuela ya kara da cewa amma kuma za su tsaya tsayin daga wajen kare duk wani hari da kasarsa za ta fuskanta koma daga ina yake. Maduro ya yi wadannan kalamai ne a gaban sabuwar majalisar tsarin mulkin kasar mai cike da cecekuce da ta sake jaddada shi a kan mukaminsa na shugaban kasa:

"Yau rana ce ta musamman, gamu a gaban majalisarmu ta kasa ta tsarin mulki, kuma gani a gabanta domin amincewa da dajarar da take da ita, kuma tana da incin kanta wajen gudanar da mulkin wannan kasa."

Shugaba Maduro ya bai wa ministan harkokin wajen kasar umarni na ya kutsa kai domin ya samo yanda zai tattaunawa da Shugaba Trump ko ta waya, ko kuma a birnin New York yayin babban zaman taron Majalisar Dinkin Duniya na ran 20 ga watan Satumba mai zuwa.