1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Venezuela da Guatemala zasu marawa Panama baya a kwamitin Sulhu

November 2, 2006
https://p.dw.com/p/Budd
Bayan kuri´a har sau 50 da babbar mashawartar MDD ta kada ba tare da wani sakamako ba, kasashen Venezuela da Guatemala sun janye takarar da suke yi na neman kujerar kasar da zata wakilci yankin Latun Amirka a kwamitin sulhu. Dukkan kasashen biyu sun amince su goyawa kasar Panama baya don ta dare kann wannan kujera. Saboda haka yanzu ba makawa Panama zata samu amincewar dukkan kasashe na babbar mashawartar. Tun a tsakiyar watan oktoba ake kada kuri´ar amma babu daya daga cikin kasashen na Venezuela da Guatemala da ta samu rinjayen kashi 2 cikin 3 da take bukata don darewa kann kujerar. Yayin da gwamnatoci masu ra´ayin canji na Latun Amirka ke marawa Venezuela baya, ita kuwa Guatemala na samun goyon bayan Amirka ne.