Van der Bellen ya lashe zaben Ostiriya | Labarai | DW | 23.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Van der Bellen ya lashe zaben Ostiriya

Tsohon shugaban jam'iyyar Green Alexander Van der Bellen ya lashe zaben shugaban kasa a Ostiriya da karamar tazara.

Sabon shugaban kasar Ostiriya Alexander Van der Bellen

Sabon shugaban kasar Ostiriya Alexander Van der Bellen

Ministan harkokin cikin gida na kasar Wolfgang Sobotka ne ya bayyana hakan inda ya ce Van der Bellen ya lashe zaben ne da rinjayen digo shida kacal. Mai shekaru 72 a duniya Van der Bellen, da ke zaman masani a kan tattalin arziki ya samu kaso 50 da digo uku cikin 100 na kuri'un da aka kada a zaben shugaban kasar wanda hakan ya ba shi damar darewa kan karagar mulkin, yayin da abokin hamayyarsa na jam'iyyar Freedom da ke adawa da manufofin kungiyar EU, Norbert Hofer ya samu kaso 49 da digo bakwai cikin 100 na kuri'un. Ko da yake ya amince da sakamakon zaben, Hofer ya ce ya yi matukar jin takaici da yadda sakamakon zaben ya kaya.