1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dan kishin kasa ya mika wuya a Ostiriya

Suleiman Babayo
December 4, 2016

Ta tabbata Alexander Van der Bellen ya lashen zaben shugaban Ostiriya inda ya kayar da dan kishin kasa Norbert Hofer mai ra'ayin rikau.

https://p.dw.com/p/2Tiox
Österreich Präsidentschaftswahlen Alexander Van der Bellen
Hoto: Reuters/L. Foeger

Zaben shugaban kasar Ostiriya ta tabbata dan taka na jam'iyyar kare muhalli Alexander Van der Bellen ya samu nasara da kusan kashi 54 cikin 100 na kuri'un da aka kada a wannan Lahadi, yayin da mai ra'ayin rikau Norbert Hofer ya rungumi kaddara. Rufe tashoshin zabe ke da wuya aka fara sanin wanda zai lashe zaben tsakanin mutanen biyu.

Shi dai Alexander Van der Bellen wanda ya lashe zaben ya kasance mai goyon bayan kungiyar Tarayyar Turai, yayin da Norbert Hofer ya nuna kansa a matsayin dan kishin kasa wanda zai kare kasar ta Ostiriya daga bakin haure da ke kwakwara suka gurbata al'adun da aka saba da su a kasar.

Sai zuwa goba Litinin kafuin samun cikekken sakamakon zaben a hukumance bayan kirga kuri'un 'yan kasar mazauna kasashen ketere.