Usama ya aikewa da Amurkawa sako
May 24, 2006Da farko dai, muryar dake kunshe a cikin kaset din bidiyon, ta fara ne da cewa, wannan sako ne daga Usama bin Mohammad bin Laden zuwa ga Amurkawa:Godiya da Aminci su tabbata ga wanda yabi kyakkawar hanya.
Usama bin Laden yaci gaba da cewa, sakon na sa ga Amurkawa sako ne daya rubuta a madadin musulmai fursunoni da Amurka ke ci gaba da tsare su,wanda
Bisa hakan yace zai fadi gaskiyar zance a game da su, duk kuwa da cewa gwamnatin shugaba Bush bata son a tsage irin wannan gaskiyar.
Usama, wanda ya aike da sakon nasa izuwa yanar giza gizan sadarwa na duniya, wato Internet a turance, ya kara da cewa zai fara ne da dan uwansa wato Zacaria Moussaoui, wanda a yan kwanaki wata kotu a Amurka ta yanke masa daurin rai da rai a gidan yari, sakamakon samun sa da laifi na hannu a cikin tsara kaiwa Amurka harin nan na sha daya ga watan satumba.
A hakikanin gaskiya a cewar Usama Bin Laden Zacaria Moussaoui baya daga cikin mutanen da suka shirya kaiwa Amurka hari kwata kwata, domin a cewar sa shine mutumin daya jagoranci shirya wannan hari, kuma daga cikin mutane 19 da suka aiwatar da shirin da kuma shirya shi babu Zacaria Moussaoui.
A cewar Usama, amsa laifin da Zacaria Moussaoui yayi na cewa yana da hannu a cikin wannan shiri, ya amsa ne kawai a sabili da takura masa da akayi na tsawon kusan shekaru hudu da rabi da aka shafe ana tsare dashi, kuma ga duk wani mai ilimi zai fahimci cewa akwai shakku a game da amsa laifin da Mossaoui yayi , musanmamma idan akayi la´akari da cewa a lokacin da aka kai harin, Zacaria Mossaoui na koyon tukin jirgin sama ne.
Usama Bin laden ya kuma tabo maganar fursunonin da ake tsare dasu a gidan yarin Guantanamo Bay,inda yake cewa dukkannin fursunonin da aka cafke a shekara ta 2001 da kuma shekara ta 2002, basu da hannu a cikin harin na sha daya ga watan satumba, sannan kuma basu da wata nasaba da kungiyyar Alqeda.
Dukkannin wadannan abubuwa dana zayyana a cewar Usama bin Laden, Gwamnatin Amurka karkashin shugaba Bush na sane da hakan ,to amma ba zasu fito fili su fadi gaskiya ba, a sabili da dalilai da suka barwa kansu sani, wanda daga cikin su shine na ci gaba da kashe biliyoyin daloli da sunan yakin Mujahiduun.
Usama Bin Laden a karshen sakon na sa ya tabbatar da cewa, ba wai ya aike da sakon bane don Amurka ta mutunta wadanda take tsare dasu din bane , illa dai kawai ya nunawa duniya irin yadda Amurka take nuna rashin adalci da kuma gallazawa ire iren wadannan mutane.
Ya zuwa yanzu dai tuni manyan jami´an tsaron Amurka suka tabbatar da cewa muryar dake kunshje a cikin kaset din bidiyon babu tababa, ta shugaban kungiyyar ta Alqeda ce, wato Usama Bin laden.