UNICEF: Masu kunar bakin wake na karuwa a Yammacin Afirka | Labarai | DW | 12.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

UNICEF: Masu kunar bakin wake na karuwa a Yammacin Afirka

Hukumar kula da jin dadin kananan yara wato UNECEF ta fadawa cibiyar Thamson Reuters Foundation da ke gudanar aiyyukan jin kai cewar, aiyyukan harin kunar bakin wake na ci gaba da bazuwa a Yammacin Afirka.

Hukumar ta kara da cewar aiyyukan harin kunar bakin waken da yanzu haka ke ci gaba da bazuwa ta hanyar yin amfani da kananan yara a mafi yawancin kasashen yammacin Afirka ciki hadda da Najeriya na ci gaba da haifar da babbar barazana.Mai magana da yawun hukumar Laurent Duviller a yayin da yake ganawa da cibiyar ya ce yin amfani da yaran musamman 'yan mata masu harin kunar bakin wake abin tayar da hankali ne kuma yana maida su wajen juya baya ga al'ummar su ta hanyar hallaka su.

Cibiyar ta ce akalla harin kunar bakin wake 44 aka samu a yammacin Afirka a shekarar da ta gabata wanda ya nininka idan aka kwatanta da hudu kacal a shekara ta 2014 musamman a kasashen Najeriya da Kamaru.Tun dai barkewar rikicin Kungiyar Boko Haram shekaru 6 da suka wuce kimanin mutane dubu 20 suka hallaka a yayin da miliyoyi suka bar muhallansu a Najeriya.