1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Unesco ta zaɓi mirganya Ana Politkovskaia a matsayin yan jaridar ta shekara

March 30, 2007
https://p.dw.com/p/BuOi

Kuma kula da ilimi da al´adu ta Majalisar Dinkin Dunia wato Unesco, ta bada lambar yabo da girmamawa, ta shekara –shekara a game da yancin yan jarida.

A shekara ban,mirganya Anna Politoskaya ta samu wannan lamba mai tarin daraja.

Hukumar Unesco, ta yanke wannan shawara a sakamakon jarimci, da sadaukarwa, da yar jaridar ta ƙasar Russia,ta nuna, wanda su ka yi sanadiyar mutuwar ta.

Ida dai ba manta ba, ranar 7 ga watan okober ne, na shekara ta 2006, wasu mutane su ka bingide Anna Politoskaya a dalili da tsage gaskiyar da ta ke, a kann al´ammuran take haƙƙoƙin bil adama, a ƙasar Russia da kuma yaƙin Tchetchenia.

Ya zuwa hukumomin Mosko da ƙungiyoyin kare haƙƙoƙin jama´a, ke zargi da kitsa wannan ta´adanci, basu bada haske ba, a game da mutuwar Anna Politoskaya.

Wannan shine karon farko, da hukumar Unesco, ta bada lambar yabo, ta yancin yan jarida, ga wani ɗan jarida mirganyi.