1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

UNESCO ta ce laifin yaki ne rusa ma'adanar tarihin Nimrud

Muntaqa AhiwaMarch 6, 2015

UNESCO ta ce rusa cibiyar adana tarihin Nimrud da IS ta yi laifin yaki ne

https://p.dw.com/p/1Emkz
Wachposten an achäologischer Stätte im Irak
Hoto: picture-alliance/Bildarchiv

Hukumar raya ilimi da al'adu ta Majaisar Dinkn Duniya UNESCO, ta ce laifin yaki ne mayakan IS suka aikata na rusa cibiyar adana tarihin nan na Iraqi da kungiyar ta yi a Nimrud na daular Assiriya.

Mahukuntan Iraqi sun ce mayakan IS sun rusa ma'adanar tarihin ne da gangan a jiya Alhamis, wajen da suka ce ke da fadin akalla kilmita 8 da ke kuma kunshe da muhimman kayan tarihi ciki har da kaburburan wasu mashahuran sarakuna.

Wata sanarwar da hukumar ta fitar yau Juma'a, ta ce babu wata hujja walau ta addini kokuma siyasa na aikata wannan barna ga wannan cibiya da ke kudu maso gabashin birnin Mosul.

Cibiyar da aka kafa shekaru dubu uku da suka gabata, kuma na biyu mafi daraja a daular ta Assiriya, tana dauke da tarihin da suka fi shafi duniya ba Iraqi kadai ba, yankin da a yanzu ke hannu mayakan na IS.