UMP ta zaɓi Sarkozy ɗan takara
January 15, 2007Jam´iyar UMP mai riƙe da ragamar mulki, a ƙasar France, ta zaɓi ministan cikin gida Nikola Sarkozy, a matsayin ɗan takarar ta, a zaɓen shugaban ƙasa, da za a gudanar a watan Aprul mai zuwa.
Nikolas sarkozy mai shekaru 51 a dunia ya kasance ɗan takara ɗaya tilo, da jam´iyar UMP ta gabatar a taron na jiya, wanda ya samu halartar dubundubatar magoya bayan UMP.
Ya kuma samu amincewa daga kashi fiye da 98 bisa 100 na yawan jama´ar da su ka kaɗa ƙuri´u.
Nikolas sarkozy, ya nasara samun haɗin kai, daga jiga-jigan wannan jam´iya, da su ka haɗa da ministar tsaro Michel Alio Marie, wadda a ka zaci ita ma, zata ajje takara.
Saidai ya zuwa yanzu, shugaban ƙasa Jacques Chirac, na matuƙar nuna ɗari-ɗari, a game da batun bada haɗin kai ga ɗan takara UMP.
Jim kaɗan bayan zaɓen da aka yi masa, Nikolas Sarkozy, ya yi jawabi kamar haka:
„A duk tsawan rayuka ta, na yi ta saƙa burrurruka, a game da yadda, za ni bautawa ƙasa ta France , a yau, kun tabbatar da matakin farko, na cimma wannan buri, a game da haka, bani da damar yin sako-sako, zan tashi tasye, tsayin daka, domin baki ɗaya mu hidda surhe daga ruwa“.
A cewar Sarkozy, cimma wannan matsayin, na bukatar gama ƙarfi da ƙarfe, tsakanin Fransawa baki ɗaya:
„Ina kira zuwa gare ku, da kuka ɗora mani wannan yauni, ku amince da cewa, daga yau, ba zan kasance ba ɗan takarar jam´iyar UMP, amma ina matsayin ɗan takara, na al´ummar France baki ɗaya, na ko wane ɓangare, daga ciki da kuma wajen ƙasar, ina bukatar haɗin kai, domin daga tutar Fransa“.
A ɗaya ɓangaren ɗan takara Sarkozy, yayi bayani da kakkausar halshe, a game da fafatar Turkiyya, na shiga rukunin ƙungiyar gamayya turai.
„A duk tsawon rayuwa ta, zan kasancewa cikkaken ɗan kishin ƙunguiyar gamayya turai, sannan a gani na ya zama wajibi, turai ta shata iyakokin ta, ta yadda ba ko wace ƙasa ba, za ta samu damar zama member, a tarayya turai, mussaman Turkiyya, wadda a ganina, kwata-kwata, bai dace ba, a karɓe ta a rukunin EU.
Yan sa´o´i ƙalilan bayan ƙaddamar da Sarkozy, a matsayin ɗan takara UMP, ya zaɓi ministan kiwon lahia, Xavier Bertran da Rachida Dati, mai bashi shawara,a matsayin sarakunan yaƙin neman zaɓe.
A yayin da ya ke maida martani, opishin yaƙin neman zaɓen yar takara jam´iyar gurguzu, wato Segolene Royal, ya nunar da cewa, babu shakka, za a fuskanci yaƙin neman zaɓe mai tsauri, ta la´akari da kalamomin ɓatanci, da Nikolas Sarkozy yayi wa jam´iyar PS.