UMP ta samu rinjaye a Makalisar Dokokin France | Labarai | DW | 18.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

UMP ta samu rinjaye a Makalisar Dokokin France

Jam´iyar UMP mai riƙe da ragamar mulki a ƙasar France ta sami gagaramin rinjaye a zaɓen yan majalisun dokoki zagaye na 2, da a gudanar jiya lahadi.

UMP ta sami jimmillar kujeru 314 daga jimmilar kujeru 577 da majalasar ta ƙunsa.

Saidai itama jam´iyar adawa ta PS, ta taka rawar gani inda ta sami kujeru 185, wato ƙarin kimanin yan majalisa kussan 40, idan a ka kwatanta da majalisaar da ta gabata.

A wannan karro,saɓanin yadda ta kasance a zaɓen shugaban ƙasa,, al´ummar France ba ta fito da himma ba, a rufunan zaɓe.

Kashi fiye da 40 bisa 100,ba su kaɗa ƙuri´a ba.

A sakamakon zaɓen, ministan ministoci, mai kula da kare mahhali da kuma ci gaban tattalin arziki, wato Alain Jupe ya sha kayi a mazaɓar sa ta Bordeaux, inda a nan take ya bayyana yin murabus daga gwamnati.

Wani amub lura awanan zabe shine dushewar tarmamuwar ɗan takara UDF, a zaɓen shugaban ƙasa wato Fransois Bayru , wanda sabuwar jama´iyar da ya girka ta Modem ta sami yan majalisa 3 rak.