1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Umaru Musa Yar'Adua ya koma gida Nigeria

.February 24, 2010

Cece-kuce tsakanin yan Nigeria dangane da halin da shugaban ƙasa ke ciki bayan komawarsa gida

https://p.dw.com/p/MAH1
Umaru Musa Yar'AduaHoto: picture alliance/dpa

Shugaba Umaru Musa Yar'Adua ya isa gida Nigeria bayan watanni uku da yayi yana jiyya a wani asibiti na ƙasar Sa´udiya. Har ya zuwa yanzu dai hukumomin Abuja basu baiyana halin da shugaban mai shekaru 58, da kuma yayi fama da cutar da ke da nasaba da zucciya yake ciki ba. Yar aduan dai bai miƙa mulki ga mataimakinsa ba kafin ya bar ƙasar. Amma majalisun ƙasar biyu sun naɗa mataimakinsa wato  Goodluck Jonathan a matsayin shugaba na rikon ƙwarya. A watan Afrilun baɗi ne za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a tarayyar ta Nigeria, amma ba´a sa ran cewa shugaba Yar'Adua zai sake tsayawa takara.