1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karshen yerjejeniyar jigilar abinci daga Ukraine

July 17, 2023

Yayin da wa'adin yerjejeniyar fitar da abinci daga Ukraine ta tekun Bahar al Asuwad ke shirin kawo karshe, an shiga fargaba kan illar rashin cimma matsaya kan tsawaita ta.

https://p.dw.com/p/4TyyA
Hoto: Andrew Kravchenko/AP Photo/picture alliance

Duk da kokarin da Majalisar Dinkin Duniya da Turkiyya suka yi a karshen makon jiya domin shawo kan Rasha, har kawo yanzu Moscow ba ta ce uffan ba a game da sabunta wa'adin yerjejeniyar wace dama da kyar da jibin goshi aka cimmat a a watan Yulin bara. 

Tun da farko dai shugaba Recep Tayyip Erdogan ya bayyana samun amincewar Rasha domin tsawaita yerjejeniyar, kafin daga bisani kakakin Kremlin ya musanta wannan batun. 

Rashar na cewa ta ki amincewa ne sakamakon rashin ba ta dama kamar Ukraine domin fitar da wadansu kayayyakinta ciki har da sinadaren hada takin zamani, sannan kuma ta ce abincin da ake fitar wa baya isa kasashen Afrika kamar yadda yerjejeniyar ta tanadar.