Uganda: Bada magani ga wanda suka jikkata | Sauyi a Afirka | DW | 27.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Sauyi a Afirka

Uganda: Bada magani ga wanda suka jikkata

Wani dan kasar Uganda da ke jagorantar kungiyar matasa ya dukufa wajen samar da magunguna da tallafawa wanda suka raunata sakamakon mumunan yaki da ya shafi gabashin kasar.

 

Miliyoyin 'yan kasar Uganda ne suka rasa rayukansu yayin yakin da aka taba yi a kasar sannan bya ga wannan anci zarafin da dama kana an yi wa mata da kananan yara fyade. Wannan ya sa Victor Ochen tare da kungiyar sa ta African Youth Initiative Network (AYINET) ke tsayawa marasa karfi da yakin ya shafa.

Shekaru 10 kenan dai da shugban kungiyar da ke tallafawa marasa lafiya bayan da ya ajiye aikin shi na Radio. Guda daga cikin wanda matsala ta shafa wato Betty Atim da ta ce ''babban sauyi da na samu a rayuwata shi ne yadda 'yan kauyenmu suka karbeni sabanin yadda aka ware ni a baya ana kyama ta ba a zama kusa da ni a coci ko a kasuwa sakamakon doyi da na ke yi."

Yanzu dai marasa lafiya da dama na farin ckin komawa cikin iyalansu ba tare da fargabar fuskantar tsana ba. Wannan ya sa ko a shekara ta 2015 shugaban wannan kungiya Ochen ya samu kyautar Nobel wanda ya zama silar samun damarmaki daga kasashen waje.