Turmutsutsu a wajen jifan shaidan a Makka | Labarai | DW | 12.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turmutsutsu a wajen jifan shaidan a Makka

Akalla mahajjata 57 ne suka rasa rayukansu a wajen jifan shedan a yau,yayinda aikin hajjin bana yake kawo karshe.

Dan jaridan Reuters yace ya kirga gawarwakin mutum 50 wasu kuma an tafi da su asibiti.

Motocin ambulance suna ci gaba da daukar wadanda suka samu rauni,yayinda sauran mahajjata suke ci gaba da jifan karshe

Wata majiya daga maaikatar harkokin waje tace ya zuwa yanzu baa san yawan wadanda suka rasa rayukansu ba.

Mahajjata kimanin miliyan 3 ne suka halarci aikin hajjin bana.

Mahukuntan saudiyan sunce bayan aikin hajjin na bana,zaa fadada gadar jamra akan kudi Riyal biliyan 4 da digo 2.