Turmutsitsi a kasar Kambodiya | Labarai | DW | 23.11.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turmutsitsi a kasar Kambodiya

Muatane da dama suka mutu a sa'ilin wani bikin ibada ta ranar ruwa a kusa da birnin Pnom Penh

default

Taron jama'a a bikin ranar ruwa

Rahotannin daga Kambodiya na cewa yawan mutane da suka mutu wanda aka tattake yayin turmutsitsi wajen bikin al'ada a wani karamin tsibirin dake kusa da  birnin Phnom Penh ya haura zuwa 350.

Kakkakin gwamnatin khieu Kan-harith ya shaidawa manema labarai cewa galibi wadanda lamarin ya rutsa da su mata ne,

Ya zuwa yanzu  babu wasu dalilai takamaimai da aka ambato da suka hadasa turmutsitsin da ya auku a kan wata gada.

To amma ana baza labarin cewa masu gudanar da  bikin  na ranar ruwa da ake yi a kowace shekara da suka yi cikar kwari a gurin, sun firgita a sa'ilin da wasu daga cikin yan shagalin suka yayata jijitar cewa gadar ta na rawa. Meng Soriya na daga cikin wadanda suka je neman yarta. " Ta ce bani da labarinta ban sani ba ko ta mutu ko a'a ba na iya yarda cewa dayawa sun mutu.

Fraministan kasar Hun sen wanda ya ce za a gudanar da bincike ya bayyana lamarin da cewa shine ta'adi mafi muni da aka samu a kasar tun zamanin gwamnatin  Khmer Rouge.

Mawallafi: Abdurahamane Hassane

Edita       :  Abdullahi Tanko Bala