TURKIYYA ZATA HADE DA EU. | Siyasa | DW | 06.10.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

TURKIYYA ZATA HADE DA EU.

TURKIYYA.

TURKIYYA.

A yau burin kasar Turkiya ya cika bayan tsawon shekaru 40,na neman shiga kungiyar gamayyar turai ,bayan da hukumar gudanar da EU din ayau ta amince fara tattauna yiwuwan hadewar turkiyyan da kungiyar.

Ayayinda Turkiyyan ke farin cikin wannan gayyata da aka mata,hukumar gudanar da kungiyar turan tayi nuni dacewa,bazata da hade da wannan kungiya ba nanda shekaru 10 masu gabatowa,tare da gargadin watsi da tattauna batun shigan Turkiyyan idan har bata cigaba da darajawa hakkin biladama da sauye sauyen democradiyya ba.Kana jamian gudanar da EU sun sake tabbatarwa sauran kasashen turan cewa,kada komai ya tsratasu idan har wannan kasa matalauciya dake da mafi yawan alummarta musulmi,ta hade da ayarin nasu na masu arziki.sai dai hukumar bata sanar da lokacin da zaa fara tattauna batun Turkiyyan ba,batu da tace ta barwa shugabannin kungiyar su zartar a taronsu na watan disamba.Inji shugaban hukumar Romano Prodi wa yan majalisar Turan.

Mr Prodi yace turai data kasance ginanniya,da tsare tsarenta masu inganci,tare da yunkurin inganta tattalin arzikinta cikin zaman lafiya,bata tsoron komai dangane da hadewanta da Turkiyya.

Shugaban fadada kungiyar EU Guenter Verheugen,a nashi bangare ya kara dacewa yana da muhimmanci a magance damuwa da tsoron alummar turan kann wannan batu,domin dole ne su bada amincewansu.

Ministan harkokin waje na Turkiyya Abdullah Gul ya kasa boye farin cikinsa wajen maraba da zartarwan wannan hukuma ,inda ya bayyana shida kasancewa wani mataki na tarihi a bangaren Turkiyyan dama sauran wakilan kungiyar 25.

Ankara na fatan zaa fara tattaunawa cikin watannin 6 farkon shekara mai zuwa,ayayinda Ministan harkokin waje na Holland Ben Bot,wadda kassarsa ce ke rike da zagayen shugaban kungiyar yace sai cikin watanni shidan karshe.

Manazarta sun yi nuni dacewa ,duk da adawa da Sustria da Cyprus sukayi kann wannan batu,bisa dukkan alamu shugaban na eu zasu amince da fara tattaunawa da Turkiyya a taron kolinsu dazai gudana a Brussels a watan Disamba.

Turkiyya wadda keda kashi 90 daga cikin 100 na yankin Asia,kana ke makwabtaka da Iraq,Iran da Syria,ta kasance cikin jerin sunayen kasashe dake neman wannan matsayi tun daga shekarata 1999.Ayayinda tun daga shekarata 1963 take neman hadewa da ayarin kungiyar kasashen turai,batu da a yan shekarun da suka gabata suka mamaye harkokin siyasan kasar.

A rahotan hukumar dai,ana iya dakatar da tattaunawa da Turkiyyan idan bata dauki matakin yaki da rashawa,dakatar da azabtarwa ta hanyar hukunci,inganta hakkin biladama ,addini da inganta rayuwar mata ba,batutuwa da prime minista Tayip Erdogan na turkiyyan yace basu dace ba,saboda babu kasar da aka taba gindaya mata waddannan sharudda saboda tana neman shiga kungiyar ta Eu.

Jamus wadda ta kasance gida wa sama da Turkawa million 2 da rabi,tayi maraba da wannan batu,Inda ministan harkokin waje Joscher Fischer yace Shugaba Gehard Schroder zai bada kuriar amincewansa a a taron kungiyar dazai gudana a watan Disamba,ayayinda shugaba Jaches Chirac na faransa yace zaa gudanar da kuriar jin raayin jamaa.

Zainab Mohammed.